Labarai A Takaice 



– Fitacciyar Jarumar masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood Rahama Sadau, ta nemi afuwar hadaddiyar kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, MOPPAN, tare da neman kungiyar ta bata damar cigaba da haskawa a masana’antar.

– A Najeriya  garin Ifon cikin jihar Ondo, wasu ‘yan fashi da makami sun fasa bankin Skye sun kwashe makudan kudi kana suka kashe ‘yan sanda uku yayinda suka yi bata kashi da jami’an tsaro.

– Tsohon Shugaban kotun daukaka karar a Najeriya, Ayo Salami ya ki karbar nadin da aka masa na jagorancin wani kwamiti da zai sanya ido kan alkalan da ke shari’ar cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da ba’a samun tsaiko wajen gudanar da shari’ar.

– Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban ‘yan gudun hijirar Sudan ta kudu na zama a Kahrtoum ba tare da muhalli ba, sakamakon rusa matsugunan su da ‘yan Sandan Sudan suka yi.

– A kasar Kenya akalla mutane Uku aka tabbatar da mutuwarsu a munanan tashin hankulan da aka samu a wasu mazabu da ke kasar wajen gudanar da zaben shugaban kasa.

– Rundunar Sojin Faransa ta sanar da kashe wasu ‘yan ta’adda 15 a kan iyakar Mali da Algeria a ci gaba da farautar masu ta da kayar baya a Yankin.

– Gwamnatin Burundi da ke fustantar bore daga ‘yan kasa ta amince da shirin yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyayan fuska domin tsawaita mulkin shugaba Pierre Nkurunziza.

– Shahararren kamfanin sada zumunta na yanar gizo Facebook, sun kammala sa hannu a wata sabuwar yarjejeniya da wani kamfanin, a yunkurin su na samar da tsarin wuta daga iska ko hasken rana. Tsarin dai zai ba kamfanin damar dogaro da kansu, wajen samar da wuta da zata bada wuta ga sabon dakin ajiye bayanai dake karamar hukumar Dixon a jihar Nebraska.

– Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta zabi tsohon mai horar da kungiyar Southampton Claude Puel a matsayin sabon mai horar da kungiyar.

You may also like