Labarai A Takaice – Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin duniya UNICEF, ya ce kashi 20 cikin 100 na haihuwar kananan yara a duniya na aukuwa ne a Najeriya.

– Wata kotun majistire dake zama a Ikeja a jihar Legas na tuhumar wani mutun mai shekaru hamsin da biyu mai suna Paul Akpederi da laifin yiwa yarshi mai shekaru goma sha shida fyade.

– A Jamhuriyar Nijar, an fara koyar da yaran makarantun firamare da harsunan gida domin inganta fahimtar karatu.

– Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban ‘yan gudun hijirar Sudan ta kudu na zama a Kahrtoum ba tare da muhalli ba, sakamakon rusa matsugunan su da ‘yan Sandan Sudan suka yi.

– Majalisar dinkin duniya ta ce nahiyar Africa tana bukatar sama da likitoci, ma’aikatan jiyya da kuma malaman makaranta miliyan 11 nan da shekara ta 2030, domin saita tattalin arziki da tsarin zamantakewar al’umma, don kaucewa kwarar bakin haure daga Afrika zuwa Turai.

– Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis yace babu wani abin da ya sake a shirin Amurka na bada kariya ga Korea ta Kudu game da barazanar makaman nukiliya da masu lizzami daga Korea ta Arewa.

– Shugaban Amurka Donald Trump Ya Bada Izinin Wallafa Takardun Bincike Dake Da Alaka Da Kisan Da Aka Yiwa Tsohon Shugaban Kasar Amurka  John F. Kennedy.

– An daure wani dan kasar Italiya mai cutar kanjamau tsawon shekara 24 a gidan yari bayan samunsa da laifin yad’a cutar da gangan ga mata har talatin ta hanyar jima’i ba tare da kariya ba.

– Ana sa ran wasan karshe tsakanin Ingila da Spain, da za’a buga ranar Asabar a kasar India, na cin kofin gasar cikin kwallon kafa ta duniya ajin ‘yan kasa da shekaru 17, ya kafa tarihin zama gasar da ta fi samun yawan masu kallo a tsawon tarihin farata a duniya.

You may also like