Labarai A Takaice  A Najeriya hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, wato EFCC, ta rungumi wata sabuwar dabara ta amfani da mawakan Kannywood don shelar yaki da cin hanci da rashawa musamman a tsakanin mata da yara.

– Akala Dakarun Najeriya uku ne suka rasu a wani harin kwantar bauna da yan kungiyar Boko Haram suka yiwa sojojin kasar a daf da dajin Sambisa.

– Fitaccen marubucin nan dan Najeriya, wanda ya taba lashe lambar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce har yanzu Shugaban kasar Muhammadu Buhari bai zama cikakken farar hula ba.

– Ana ci gaba da nuna damuwa game da yiwuwar barkewar cututtuka sakamakon amfani da gurbatattcen ruwa a Kisangani, birni na uku mafi girma a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo saboda katsewar wutar lantarki da ruwan sha.

– Masu hakar ma’adinai a Saliyo sun hako wani diamond wanda nauyinsa ya kai karat 476, kuma an ce shi ne diamond na 29 ma fi  girma da aka gano.

– Hukumomin kare hakkin dan adam a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, sun sanar da fara sauraron karar mayakan ‘yan tawayen da ke gabashin kasar 18, da ake zargi da cin zarafin kananan yara mata 46, ciki har da ‘yar watanni 18 da haihuwa.

– Gwamnatocin kasashen Uganda da Tanzania, sun yi alla wadai da matakin, kaddamar da bincike kan zargin gwamnatin Burundi da aikata laifukan yaki da kotun kasa da kasa ICC ta yi, inda suka ce hakan zai iya jefa kasar, dama yankin gabashin nahiyar Afrika cikin sabon rikici.

– Tawagar masu sa’ido da majalisar dinkin duniya ta tura Sudan ta Kudu, sun shaidawa kwamitin tsaron majalisar cewa, gwamnatin Salva Kiir tana amfani da abinci a matsayin makamin yaki.

– A kasar Iraki hukumomin kasar sun ce sun gano wasu manyan kaburarrika wadanda suke dauke da gawawwakin mutum 400 a wani wuri da ke kusa da garin Hawija.

– Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta fitar da sanarwarta ta farko a hukumance kan ziyarar da Trump yake a yankin Asiya, tana mai cewa “Wannan ziyara ce ta mai son yada yake-yake musamman ga kasarmu, a kokarin dakile mana garkuwarmu ta Nukiliya.

– Akalla ‘yan yankin Catalonia dubu 750 ne suka gudanar da zanga-zanga, a birnin Barcelona, domin neman gwamnatin Spain ta saki jagororin yankin da har yanzu take tsare dasu, sakamakon rawar da suka taka wajen fafutukar neman ballewar yankin daga kasar.

– Sojin Iraqi sun kaddamar da wani sabon farmaki domin kwato garin Rawa, da ke hannun mayakan IS, wanda shi ne karamin yanki na karshe da ke karkashin ikon kungiyar.

– Shugaba Trump da Koriya ta Arewa sun sake dawo da fadan cacar bakin da suke yi kan shirin makamin nukiliya na gwamnatin Pyongyang.

You may also like