Labarai A Takaice – A Najeriya dan takarar Jam’iyyar APGA, Willie Obiano, ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudancin kasar.

– A Najeriya mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya ce babu yadda Boko Haram zata habaka daga gari daya har zuwa garuruwa da dama a Nigeria da wasu kasashen ba tare da samun haramtattun kudade ba.

–  A kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya gabatar da jawabi ta kafar talabijin din kasar, amma ba tare da ya ambaci cewa ya sauka daga shugabancin kasar ba, kamar yadda jami’iyar ZANU-PF da ta koreshi daga shugabancinta ta bukata.

– Hukumomi a Jamhuriyar Niger sun bayyana takaicinsu game da cinikin mutane a matsayin bayi, abinda kasart ace zata mike tsaye har sai ta ga bayan wannan mummunar kasuwancin.

– A ranar Larabar da ta gabata ne jirgin karkashin ruwa kirar Jamus ya bace a wani yanayi mara kyau, an kawo jiragen ruwa da na sama daga wasu kasashe dake taimakawa wurin ceto jirgin dake dauke da mutane 44. 

– Bayan wata girgizar kasa da ta auku a New Caledonia dake yankin kudancin Pacific masu kula da irin yanayin da girgizar kasar ta haddasa suna gargadin yiwuwar aukuwar ambaliyar tsunami.

– Ministocin harkokin waje na kasashen Larabawa suna gudanar da taron gaggawa a hedikwatar kungiyar kasashen Larabawan da ke birnin Alkahira.

– Kungiyar tarayyar turai Eu ta ce zata zaftare kudaden da take bai wa kasar Turkiya a matsayin taimako, sakamakon yadda gwamnatin Recep Tayyib Erdogan, ke kokarin karya tsarin Dimokradiyya.

– Tsohon kociyan Manchester United David Moyes ya fara aikinsa da West Ham da rashin nasara, inda Watford a gidanta ta doke su da ci 2-0, a wasansu na Premier, jiya Lahadi.

You may also like