Labarai A Takaice – Gwamnatin Jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya na shirye-shiryen mayar da gidan tsohon jagoran kungiyar Boko-Haram Muhammad Yusuf zuwa gidan tarihi. Matukar shirin ya kammala a kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar zai taimaka gaya wajen samar da kudaden shiga baya ga kasancewa Izina da kuma wadanda za su taso nan gaba.

– Mai alfarma sarkin Musulmin Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci gwamnatin kasa da ta hanzarta binciko wadanda ke da hannun a kissan mummuken da aka yiwa Fulani makiyaya a yankin Gembu dake jihar Taraba,da kuma na kwanakin nan a Numan inda rayukan kananan yara fiye da hamsin suka salwanta.

– Rundunar sojin Najeriya ta ce akalla sojin ta uku ne suka mutu yayinda karin wasu uku kuma suka jikkata a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai kansu a ranar Asabar a garin Magumeri mai nisan kilomita 50 da birnin Maiduguri.

– Jam’iyyar Liberty a kasar Liberia tace zata daukaka kara zuwa kotun koli kan zargin cewar an tafka magudi a zaben shugaban kasar da akayi ranar 10 ga watan Oktoba.

– Masana kimiyya na gargadin cewa tafkin Victoria ,wanda shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrika , na fuskantar barazanar gurbacewa.

– Kasar Saudi Arabia ta fara gudanar da wani taron kasashen Musulmi 40 na duniya kan yadda za’a kulla yarjejeniyar yaki da ta’addanci.

– Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi yace yana kan hanyar cimma burin sa na kammala rayuwar sa na kwallon kafa a kungiyar Barcelona, bayan ya sanya hannu kan wata sabuwar kwangila.

– Chelsea ta bayar da hakuri ta kuma yi hayar motocin safa suka dauki magoya bayanta da suka je kallon wasanta da Liverpool saboda jirgin kasa da ta yi haya musamman domin jigilarsu ya yi latti, har suka rasa ta yi a tasha.

– Arsenal ta ci gaba da yin manyan wasanninta har zuwa goma ba tare da an doke ta ba, inda ta buge Burnley da ci 1-0 a wasan Premier na 13, da nasara a 7, da canjaras a 3.

You may also like