Labarai A Takaice  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kwaso daukacin yan Najeriya da suka makale a kasar Libya inda yanzu haka ake sayar da baki bakaken fata.

– Najeriya na kokarin bin kadi mutuwar wasu mata 26 ‘yan Afirka a cikin tekun Bahar Rum, tekun da ya lakume rayukan dubban bakin haure musamman ma daga Afrika.

– A Najeriya ganin yadda aka kasa tsaida yawan fada tsakanin manoma da makiyaya, a jahar Adamawa an kafa rundunar shiga tsakanin manoma da makiyaya idan takaddama ta barke a tsakaninsu.

– Bayan da aka samu labarin wata tabargaza ta cinikin bakaken fata a matsayin bayi a kasar Libiya hankalin magabatan bakaken fata ya tashi a fadin Duniya. Don haka a matsayin Shugaban kasar bakaken fata mafi girma a duniya, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na da hujjar tinkarar al’amarin gadan-gadan.

– Shugabannin kasashen nahiyar Afirka da takwarorinsu na turai, suna gudanar da wani taron koli a Abidjan, babban birnin Cote d’ Ivoire domin tattauna matsalolin da suka shafi nahiyoyin biyu musamman kan batun kwararar bakin haure zuwa turai.

– Akalla mutum 50 ‘yan bindiga suka kashe a gabashin Sudan ta Kudu, harin da ke kasance irinsa na baya-bayanan da ake fuskanta a yankin da ake yawaita samun rikicin kabilanci.

– Ana sa ran wakilan gwamnatin kasar Siriya zasu je Geneva inda zasu yi ganawar neman samar da zaman lafiya wadda Majalisar Dinkin Duniya zata jagoranta, da zummar kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 7 ana yi.

– Bayan gwajin wasu makamai masu dogon zango da Koriya Ta Arewa ta yi, Amurka ta sake yi ma ta kashedi ta cewa daina shirin daukar Dala ba gammo saboda ba za ta lamunta da ganin makamai masu hadari a hannun kasa irin Koriya Ta Arewa ba.

– Kotun duniya da ke birnin Hague ta dakatar da zaman sauraren shari’ar Slobodan Praljak da ake zargi da aikata laifukan yaki a Bosnia bayan ya kwankwadi guba. Mr. Praljak ya kwankwadi gubar ne bayan Kotun ta goyi bayan hukuncin daurin shekaru 20 da aka yanke ma sa.

You may also like