LABARAI A TAKAICE Shugaban Najeriya Muhammad Buhari na cikin shugabannin da suka kasance a taron kasa da kasa da ya gudana a Jordan akan musabbabin dake haddasa ta’addanci da wasu miyagun dabi’u da yadda za’a yakeso. 

– Shugaban jam’iyyar PDP Ahmed Mohammed Makarfi ya ce ba za su ba wa Atiku Abubakar takarar shugabancin kasar kai tsaye ba, sai dai idan ‘yan jam’iyyar ne suka tsayar da shi.

– Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin  Najeriya, na cewa wani rikici mai nasaba da kabilanci da kuma rikicin gonaki ya barke a wasu  kauyuka da ke kusa da garin Numan,  ya jawo asarar rayuka da dukiya.

– Gwamnatin Najeriya ta ce, kasar Switzerland na shirin maido ma ta da Dala miliyan 321 da ake zargin marigayin tsohon shugaban kasar a mulkin soja, Janar Sani Abacha da wawushewa daga asusun gwamnati.

– Babbar kungiyar nakasassu ta Damagaram ta koka da yadda ake nuna musu wariya game da kayayakin da suke kerawa, duk da kiraye-kirayen da ake musu na su daina bara su rungumi sana’a.

– Jam’iyar tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ta tabbatar jiya Litinin cewa an kashe shi, yayin da ake yayata wani faifan bidiyo a kafofin sadarwa da ake cewa gawarsa ce.
– Daya Daga cikin fitattun jaruman fina-finan India na da Shashi Kapoor ya mutu yau litinin yana da shekaru 79 a duniya.

– Shugaban Amurka Donald Trump ya jinkirta bayyana matsayinsa dangane da shirin da Isra’ila ke yi na dauke fadar gwamnatin kasar daga Tel Aviv Zuwa birnin kudis, a wata sanarwa da ta fitar.

– Kotun kolin Amurka ta bai wa gwamnati damar fara aiki da kudurin dokar da ke hana wa ‘yan asalin wasu kasashe 6 na Musulmi damar shiga kasar kafin yanke hukunci dangane da karar da wasu jihohi suka daukaka a wannan batu.

– Dan wasan Brazil Neymar Da Silva ya bayyana farin cikinsa na rashin hada kasarsa da Najeriya a cikin rukuni guda a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci a badi.

– Tsohon dan wasan Najeriya, Tijjani Babangida ya ce, kar a kuskura a tirsasa wa Vincent Enyeama dawowa cikin tawagar Super Eagles don tsaren raga a gasar cin kofin duniya a Rasha bayan ya yi ritaya shekaru biyu da suka wuce.

You may also like