LABARAI A TAKAICE – A Najeriya Shugaban Hukumar zaben kasar Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, a ranar 16 ga watan Fabrairun 2019 ne za a yi zaben shugaban kasar da ‘yan majalisar tarayya idan Allah Ya kai mu.

– Jigon jam’iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya ce jam’iyyar APC ba za ta iya gudanar da babban taro ba tare da rudani ba.

– Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya, NEMA, ta fara kai kayayyakin tallafi ga wadanda rikicin makiyaya da ‘yan Bachama ya shafa a jihar Adamawa.

– Wasu daga cikin ‘yan takarar da suka nemi kujerar shugaban jam’iyar PDP mai adawa a Nijeriya sun ce ba su amince da sakamakon zaben da ya bai wa Prince Uche Secondus nasara ba.

– A Sudan an janye tuhumar da ake yi wa wasu mata 24 wadanda aka kama saboda sun saka wando a wani taron liyafa da aka yi kusa da Khartoum babban birnin kasar.

– Hukumomin lafiya a Ghana sun tabbatar da cewar cutar murar tsuntsaye ita ce ta yi sanadiyyar mutuwar wasu dalibai hudu a babbar makarantar sakandire ta Kumasi Academy.

– Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya buƙaci Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya daina gine-gine a yankunan Falasɗinawa da kuma ƙaddamar da tattaunawa domin kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

– Yan sanda a Mumbai na kasar India, sun kama wani mutum da ake zargi da cin zarafin wata jaruma ‘yar kimanin shekara 17 da haihuwa a lokacin da suke cikin jirgin sama.

– Manchester City ta yi nasara a kan abokiyar hamayyarta Manchester United a wasan da suka yi gumurzu ranar Lahadi inda suka tashi wasan 2-1.

You may also like