LABARAI A TAKAICE 



– Matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) a jihar Gome sun yaba da sabon shirinnan na gwamnatin tarayya wanda ke koyawa masu yiwa kasa hidima sana’oin hannu da aka yiwa lakabi da Skills Acquisition Developemnet Programme ko (SAED) a takaice.

– Rahotanni daga Najeriya na cewa shugaban kwamitin gudanarwar jam’iyar PDP na rikon kwarya ya mika ragamar tafiyar da jam’iyar ga zababbun shugabannin jam’iyar.

– Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana Jam’iyyar PDP a matsayin sabuwa, in da ya bukaci ‘yan Najeriya su yi mu su afuwa kan kura-kuran da suka tafka a matsayinsu na ‘yan Adam.

– An bude taron kasashen da ke gabar tekun Guinea a Legas domin tattauna matsalolin da ke addabar yankin.

– A karon farko hadakar kungiyoyi farar hula na jamhuriyar Niger, da murya daya ta fito ta kalubalacin kasasfin kudin kasar na shekarar 2018 mai zuwa saboda wasu abubuwa da taek zargin kasafin ya kunsha kuma zai yiwa talakawa illa.

– Kungiyar Kasashen Afrika AU ta yi gargadin cewar akalla mayakan ISIS 6,000 ake fargabar cewa za su koma nahiyar Afrika bayan an yi nasarar murkushe su a kasashen Iraqi da Syria.

– Aƙalla shugabannin ƙasashen duniya 50 ne ake sa ran za su halarci taro a birnin Paris, a daidai lokacin da aka cika shekaru biyu da ƙulla yarjejeniyar duniya kan ɗumamar yanayi wadda kasashe 195 suka sanya wa hannu.

– Kasashen Musulmi da suka hada da Lebanon da Indonisia da Morocco da Masar sun gudanar da zanga-zanga a karshen mako don nuna adawa ga matakin shugaban Amurka Donald Trump na ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

– Frayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa yana da yakini kasashen turai za su maida ofisoshin jakadancinsu zuwa birnin kudus.

You may also like