LABARAI A TAKAICE – Al’ummar Nijeriya na ci gaba da fuskantar karancin man fetur a sassan kasar daban-daban, lamarin da ke ci gaba da haddasa cunkuson ababen hawa a gidajen sayar da man baya ga karuwar farashinsa sabanin yadda gwamnatin kasar ta sanya kan Naira 145 kowace lita guda.

– Gwamatin Nijeriya ta ƙaddamar da wani shiri na lalubo hanyar magance tashin hankalin da ke haddasa asarar rayuka tsakanin Fulani makiyaya da manoma a ƙasar.

– An sami bullar cutar sankarau a Nijar har wasu sun rasu. Sai dai hukumomin kiwon lafiyar kasar sun ce suna iyakar kokarinsu na ganin sun shawo kan lamarin cutar.

– Majalisar Dokokin Isra’ila ta amince da matakin ƙuntatawa ‘yan ciranin da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, abin da zai bai wa gwamnati damar aiwatar da shirinta na mayar da kimanin baƙi dubu 40 zuwa nahiyar Afrika. Gwamnatin ta bayyana Rwanda da Uganda a matsayin ƙasashen da za ta jibge bakin na Afrika.

– Kamfanin Apple ya sayi manhajar tantance wakoki da ake kira Shazam wadda aka kirkiro a Birtaniya, wanda ke zama babban ciniki da Apple ya taba yi.

– Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fadawa masu zuba jari a kasashen duniya sama da 200 da shugabannin duniya 50 cewa ba a samun nasara a yakin da ake da sauyin yanayi.

– Doug Jones ‘dan jam’iyyar Democrat ne ya lashe zaben da aka gudanar na musamman don cike gurbin kujerar Majalisar Dattijai a jihar Alabama dake kudancin Amurka.

– Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tunatar da takwaransa na Amurka Donald Trump game da sauke nauyin da ya rataya a wuyansa bayan ya janye ƙasarsa daga yarjejeniyar ɗumamar yanayi da aka cimma shekaru biyu da suka gabata a birnin Paris.

– A bangaren cinikayyar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya wadda za’a bude a watan Janairu dubu biyu da sha takwas, 2018, Newcastle United tace tana bukata dan wasan Manchester United, Luka Shaw, amma bata son biyan fam miliyan £20 kamar yadda kulob dinsa ke nema.

You may also like