LABARAI A TAKAICE – A Najeriya Wata Kotun soji da ke zaman ta a Maidugurin arewacin kasar ta yankewa wani soja hukuncin kisa saboda samun sa da laifin kashe fararen hula.

– Hukumomi tsaron kasar Kamaru sun ce wasu ‘yan bindiga da suka fito daga yankin da ke amfani da yaren English masu neman ballewa sun kai hari kan wani kauye tare da farwa jami’an Sojin kasar.

– Jam’iyyar ZANU-PF a Zimbabwe ta tsayar da shugaban kasar mai-ci Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda zai tsaya mata takarar shugabancin kasa a zaben kasar da za a gudanar cikin shekara mai zuwa.

– Wani rahoton bincike ya bayyana cewa, kananan yara kusan 500 ne suka rasa rayukansu sakamakon taka nakiyoyi a bara. Rahoton ya ce, akala mutanen da suka mutu ta wannan hanyar a 2016 sun kai dubu 8 da 605, wanda shi ne adadi mafi girma da aka gani tun shekarar 1999.

– Shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya kira kasashen musulmai na Duniya da su gudanar da zanga-zanga nuna goyan baya zuwa Falesdinawa dangane da matakin Shugaban Amurka na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra’ila mako daya da ya gabata.

– Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da shiga mataki na gaba a tattaunawar da suke kan makomar alakarsu da Burtaniya da ke shirin ficewar daga cikinsu. Sai dai sun yi gargadin cewar ganawan wannan lokaci zai yi tsauri sama da na farko kafin su kai wannan matsayin.

– Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka sama da rabin ‘yan gudun hijirar Syria da suka samu mafaka a kasar Lebanon na fama da tsananin yunwa, yayin da akasarin su na rayuwa cikin tsananin talauci.

You may also like