- A Nijeriya kungiyoyin kare hakkokin Musulmi na kasar sun yi kira ga hukumar makarantar koyon aikin lauya ta kasa da ta gaggauta tabbatar da Malama Firdausa Amasa a matsayin cikakkiyar lauya.
- Nijeriya ta sami kyawun amfanin gona da kuma karuwar hako gangunan man fetur miliyan biyu da rabi a rana, wanda hakan ya kara fito da Najeriyar daga komadar tattalin arzikin data fada a baya.
- Shahararren kamfanin sada zumunta na Facebook ya dauki mataki kan korafe-korafen satar fasaha da amfani da aikin wani ba tare da izini ba, kamfanin ya sanar da cewa cikin watannin shidan karshen shekarar 2017 ya cire wasu abubuwa da mutane ke kafewa kusan Miliyan uku a dandalinsa.
- Mambobin bangarorin da ke rikici a Sudan ta Kudu sun hadu a wani taro da ake gudanarwa wanda ake fatan za a samar da yajejeniyar tsagaita wuta zuwa ranar Juma’a.
- Majalisar Dokokin Uganda jiya talata ta dage zaman da ta shirya domin ci-gaba da mahawara kan shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska domin bai wa shugaba Yoweri Museveni damar ci-gaba da zama a kan karagar mulki.
- Kotun Afrika ta Kudu ta bayar da belin wani dillalen makamai dan kasar Netherlands Guus Kouwenhoven, wanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 10 gidan yari bayan samun sa da laifi a yakin basasarar Liberia da kasar Guinee kama daga shekara ta 1991 zuwa 2001.
- Majalisar dattawan Amurka ta amince da sabuwar dokar rage haraji a kan manyan kamfanoni, daya daga cikin alkawurran da Donald Trump ya dauka a lokacin yakin neman zabensa.
- Sarki Abdallah na Jordan ya gana da Fafaroma Francis inda suka tatattauna kan matsayin Birnin Kudus da kuma matakin da Amurka ta dauka.
- Kasar Saudi Arabia ta ce ta kakkabo wani makamin roka da ‘Yan Tawayen Huthi da ke Yemen suka harba zuwa Riyadh.
- Baban taron Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa na ba sa banba ranar Alhamis domin nazarin shawarar Amurka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila.
- Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya bayyana nadamarsa ga cijewar shirin shiga tsakanin bangarorin adawar Syria a Geneva da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a makon da ya gabata.