LABARAI A TAKAICE 


  • Wata Kotu a kasar Italiya ta bukaci gurfanar da manyan kamfanonin hako man Eni da Shell saboda samun su da hannu wajen bada cin hanci ga jami’an gwamnatin Najeriya dangane da cinikin wata rijiyar mai da aka yi cinikin ta akan Dala biliyan 1 da miliyan 300.
  • Tsohon shugaban Mali Amadou Toumani Toure da ke gudun hijira a Senegal tun 2012, zai koma kasar nan da zuwa karshen wannan mako, a wata sanarwa da fadar Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita.
  • Hukumar tara bayanan sirri ta Rasha FSB, ta ce sama da ‘yan asalin kasar 4.500 ke gudanar da ayyukan ta’addanci a karkashin kungiyoyi daban daban da ke yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka.
  • Bayan watsin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi da daftarin da Masar ta gabatar da ke neman hana Amurka ayyana Quds a matsayin fadar gwamnatin Isra’ila, a gobe Alhamis za a soma zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya wanda babu damar hawan kujerar na-ki zai tattauna a kan wannan batu.
  • Yan sanda a kasar Australia sun ce wani mutum da ya kutsa cikin jama’a da motarsa a Melbourne, birni na biyu mafi girma a kasar, ya yi haka ne da gangan.
  • An kammala yakin neman zaben da ake shirin gudanarwa gobe alhamis a yankin Catalonia da ya yi yunkurin ballewa daga Spain, lamarin da ya kai ga cafke wasu shugabannin yankin yayin da wasu suka yi hijira.
  •  Rahotanni Daga kasar Amurka sun ce yanzu haka ‘Yan Sanda na tsare da wasu karnuka guda biyu da ake zargi da kashe uwargidan su, Bethany Lynn Stephens, mai shekaru 22 a Jihar Virginia.
  • Yan sanda a kasar Australia sun ce wani mutum da ya kutsa cikin jama’a da motarsa a Melbourne, birni na biyu mafi girma a kasar, ya yi haka ne da gangan.
  • Mai horar da kungiyar kwallon kafa na kasar Perou Ricardo Gareca ya bayyana cewa ya na da yakini cewa kungiyar kwallon kafar Faransa za ta taka gaggarumar rawa a gasar cin kofi kwallon kafar Duniya da za ta gudana a Rasha a shekarar 2018.

You may also like