- A Nijeriya Majalisar wakilan kasar ta ce sai ta kammala bin diddigin yadda gwamnati ta kashe kudaden da aka ware a cikin kasafin kudin bana domin tsarin nan na samar da ayyuka ga ‘yan Najeriya wato N-Power da kuma baiwa talakawa da marasa karfi naira dubu biyar kowane wata kafin su amince da kudin da aka tanada a kasafin kudin badi.
- A Najeriya Wasu masu ababen hawa sun koka akan yadda suke shan wahala kowacce shekara musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti saboda matsalar mai, amma da lokacin ya wuce sa man ya wadatu.
- Majalisar Dinkin Duniya da gagarumar rinjaye ta yi watsi da matsayin Amurka na bayyana Birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila. Duk da barazanar janye tallafi da Amurka ta yiwa kasashen duniya, kasashe 128 suka kada kuri’ar watsi da matsayin na Amurka.
- Gwamnatin Sudan Ta Kudu da kungiyoyin mayaka sun rattaba hannu kan yarjajjeniyar tsagaita wuta jiya Alhamis, a yayin tattaunwar zaman lafiya a kasar Habasha.
- Firaministan Faransa Edouard Philippe ya jagoranci bikin rufe tattaunawa kan yadda za a inganta harkar noma da samar da abinci bayan share tsawon watanni 5 ana tattaunawa.
- Yan awaren yankin Catalonia a jiya alhamis sun yi nasarar rike rinjayen da suke da shi a majalisar dokokin yankin, al’amarin da ya sake jefa kasar Spain cikin rashin tabbas, tun bayan yukurin yan awaren dake ci gaba da daukar hankali a nahiyar turai.
- Majalisar dokokin Rasha ta amince da wata yarjejeniya tsakanin kasar da Syria wadda za ta bai wa Rasha damar bunkasar sansanin sojin ruwanta da ke a Tartus na Syria.
- Chelsea tace tana da sha’awar dauko Rossy Barkley mai shekaru 24 daga Everton da kuma Thomas Lemar mai shekaru 22, na Monaco a watan Janairu.
- Kotun da’a daga hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta sassauta hukuncin dakatar da Paulo Guerrero dan wasan kasar Perou na shekara daya da ta yi.