Labarai A Takaice 


  •  A Najeriya ana ci gaba da kokawa bisa karancin manfetur, wasu daga cikin ‘yan kasuwar da ke shigar da man daga kasashen ketare, sun bukaci gwamnatin kasar da ta tallafa, wajen saukaka musu samun dala bisa farashi mai rangwame, musamman domin basu damar ci gaba da shigo da man.
  •  Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce babban aikin da ke gaban shugaban Nijar Mahammadou Issofou a halin yanzu shi ne gudanar da karbabben zabe a shekara ta 2021.
  • Korea ta Arewa ta ce matakin da kwamitin tsaron Majalisar dinkin duniya ya dauka na sake kakaba mata takunkumi, tamkar shelanta yaki ne a kanta, haka zalika mataki ne da aka shirya mugun nufi ga tattalin arzikin kasar.
  • Gobara ta barke a gidan ajiye dabbobin daji na birnin London, inda wani ma’aikaci ya sami rauni yayin da kuma wata dabba mai dogon hanci da ake kira aardvark ta mutu.
  • A kasar India yan sanda sun ce wata motar bus mai dauke da mutum 50 ta rikito daga kan gada a arewacin Indiya, a kalla mutum 32 suka mutu.
  • Jami’an ceto a Philippines suna ci gaba da aikin neman daruruwan mutanen da ambaliyar ruwa ya rutsa da su a kudancin kasar, sakamakon guguwar da ta afkawa yankin.
  • Gobarar dajin da ta lalata sama da gidaje 700 a Carlifornia, ta zama mafi muni da ta taba aukuwa a jihar.

You may also like