Labarai A Takaice 


 • A Najeriya NNPC, na aiki da jami’an “Civil Defence” domin damke masu karkatar da Man fetur, da kuma daukar matakai kan masu sayarda Man fiye da ka’idar gwamnati.
 • A Najeriya rundunar ‘yansandan kasar ta yi gagarumin nasarar damke wasu hamshakan miyagu wajen 30 bayan da su ka aikata manyan laifuka ciki har da kashe wani Bature saboda ba a ba su kudin fansan da ya kai miliyan 70 ba.
 • Rahotanni daga Najeriya sun ce dan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi hadari a babur daren a Abuja, kuma ya samu raunuka a jikin sa harda karaya a kafarsa.
 • Kasar Amurka ta amince ta saidawa Najeriya jiragen yakin sama 12 kirar Super Tucano A-29, domin yaki da kungiyar Boko Haram.
 • Shugaba Buhari tare da Uwargidarsa suna godiya da dimbim addu’o’in ‘yan Najeriya ga dansu da ya gamu da hadari.
 • A jihar Kaduna Wata kungiyar fafutukar zaman lafiya a jihar ta Global Peace Foundation ta yi kira ga hukuma da gabatar da duk masu tada rikici a cikin jihar gaban shari’a saboda sauran jama’a su dauki darasi.
 •  ‘Yan majalisar adawar Kenya na kalubalantar gwamnati akan dalilin faduwar dalibai dayawa a jarrabar gama sakandare ta wannan shekarar.
 • Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana farin cikin sa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar Liberia zagaye na biyu cikin kwanciyar hankali.
 •  Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce yunkurin samar da zaman lafiya ta fuskar siyasa ba zai taba yiwuwa ba a Syria, muddin shugaban kasar Bashar al-Assad na karagar mulki, wanda ya bayyana a matsayin dan ta’adda.
 •  Dan wasan Gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Harry Kane, ya kafa tarihi a bangaren jefa kwallaye a gasar firimiya lig ta kasar Ingila bisa tsarin kalandar shekara shekara.
 •  Kungiyar Liverpool ta sayi dan wasan baya na kungiyar Southampton Virgil Van Dijk a kan fam miliyan 75, abinda ya bashi damar zama dan wasan baya mafi tsada a duniya.

You may also like