Labarai A Takaice 


  • A Najeriya, rundunar sojin kasar ta ce ta dakile wani hari da wasu ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi kokarin kai wa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
  • A Abuja wata rigima ta barke tsakanin wasu majiya karfi a Karamar Hukumar Bwari da ke yankin Birnin Tarayyar Najeriya, wanda ya yi sanadin mace-mace da asarar dukiyoyi na miliyoyin naira. Hukumomi dai sun ce sun kwantar da kurar.
  • Gwamnatin Najeriya ta jaddada cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen karancin mai da ake fuskanta.
  • Kungiyar bayar da agaji ta Medicins Sans Frontiers ta ce matsalar tsaro a Jamhuriyar Africa ta tsakiya na kara tabarbarewa.
  • Kungiyar bayar da agaji ta Medicins Sans Frontiers ta ce matsalar tsaro a Jamhuriyar Africa ta tsakiya na kara tabarbarewa.
  • Tsohon shugaban Mali wanda sojoji suka kifar, Amadou Toumani Toure ya koma kasar a jiya lahadi bayan share sama da shekaru 5 a kasar Senegal, inda ya samu gagarumin tarbo daga al’ummar kasar da kuma shugaba Ibrahim Boubacar Keita.
  • A Congo mayakan Mai-Mai sun banka wuta a gidan Shugaba Joseph Kabila dake yankin Mesuienne a gabacin kasar,an bayyana cewa sun kwashe kayyaki da dama.
  •  Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Jerada da ke arewacin Morocco don nuna fushi dangane da mutuwar mutane biyu a wata mahakar ma’adinai.A yau talata al’ummar Liberia ke sake gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda za’a fafata tsakanin mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai da Sanata George Weah.
  • Hukumar zabe a Rasha ta yi watsi da bukatar da jagoran ‘yan adawa Alexei Navalny ya gabatar domin tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na shekara mai zuwa don fafatawa da Vladimir Putin.

You may also like