Labarai A Takaice 


  •  Gwamnatin Najeriya ta kare kanta daga zargin cewa rashin iya aiki ne ya sanya bayyanar sunayen mutanen da suka mutu a jerin sabbin nade-nade na mutane dubu 1,258 da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi, na shugabannin hukumomin gwamnatin kasar da sauran ma’aikatu.
  •  Shugaban ƙasar Zambia Edgar Lungu ya bukaci sojoji su taimaka wajen kawo ƙarshen yaduwar cutar kwalara, wadda ya zuwa yanzu ta hallaka mutane 41 a kasar.
  • Gwamnatin Jamhuriyar Congo, ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin katse layukan waya da na Intanet a baki dayan kasar, yayinda ‘yan adawa ke shirin fara gagarumar zanga-zanga.
  • Hukumar tace fina-finan kasar India ta ce babu wata matsala a tattare da fim din Padmavati wanda masana’antar kasar ta Bollywood ta shirya shi.
  •  Gwamnatin Nepal ta haramtawa mutane hawa tsaunukan da ke kasar su kadai, ba tare da taimakon jami’ai ba, musamman ma tsauni mafi tsawo a duniya wato Everest.
  • Akalla mutane biyu daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Iran sun mutu a garin Dorud da ke yammacin kasar, yayinda aka shiga rana ta uku da fara bore.
  •  Masu zanga-zanga a Iran sun bijire wa gargadin da gwamnati ta yi, inda suka ci gaba da fitowa a titunan ƙasar domin nuna fushin su kan matsi na tattalin arziki.

You may also like