- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya alkawarta sanya kafar wando daya da mutane da suka haifar da tsananin wahalar man fetir da ya durkusar da hidindimun al’ummar kasar.
- Rahotanni daga jihar Rivers da ke kudancin Nigeria sun ce wasu ‘yan bindiga da aka gaza sanin manufarsu sun kashe Mutane 21 da ke hanyar komawa gida kafin wayewar garin jiya littini bayan sun kwana suna addu’o’i a Coci.
- Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe Sarkin Gwantu wato Etum Numana a karamar hukumar Sanga, da ke jihar Kaduna a tarayyar Najeriya.
- Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci Shugaban kasar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo Joseph Kabila ya sauka daga mulki kamar yadda aka yi da shi cikin yarjejeniyar shekara ta 2016.
- Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce dole ne gwamnati ta bayar da kafar yin suka daga ɓangarori daban-daban, sai dai ya ce ba za a lamunci tayar da rikici ba.
- Kafar talabijin ta kasar Iran ta tabbatar da cewa mutane 10, daga cikin dubban masu bore a kasar sun hallaka yayinda suke ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati.
- Kasar Korea ta Kudu ta fitar da wani tsarin tattaunawar sulhu da makwabciyarta Korea ta Arewa a ranar 9 ga wannan wata na Janairu.
- Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Sir Alex Ferguson, ya taya kocin Arsenal Arsene Wenger, murnar kafa sabon tarihin zama mai horarwa daya zarta takwarorinsa yawan jagorantar wasanni gasar Premier.
- Mai horar da kungiyar Arsenal Arsene Wenger, ya zargi jami’an da ke shirya wasannin gasar Premier ta Ingila, da nuna son kai ciki kakkausan harshe.