Labarai A Takaice 


  • A jihar Kaduna ‘Yan bindiga sun sace Amurkawa biyu da wasu ‘yan kasar Canada su biyu a cikin Jihar dake yankin tsakiyar Najeriya.
  •  Gwamnatin Najeriya tayi afuwa ga wasu daurarru guda 368 dake tsare a gidan yari na Kurmawa dake Kano, a wani mataki na rage cunkoso a gidajen yarin kasar.
  • Kungiyar matasan kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo OYC, ta umarci baki dayan Fulani makiyaya da su fice daga yankunansu da ke kudu maso gabashin Najeriya.
  • Jaruma Rahma sadau ta bukaci masoyanta da masu ruwa da tsaki su yi hakuri dangane da abin da ya faru a baya, inda ta ce idan abu ya faru afuwa ya kamata a yi mata kamar yadda ake wa kowane dan’adam ta kuma kara da cewa kamar sauran ‘yan adam, ita ma zata iya yin kuskure.
  •  Mutane 12 sun hallaka a harin da wasu ‘yan kunar bakin wake biyu suka kai a garejin Muna da ke birnin Maiduguri.
  • Gwamna Nasiru El-Rufai, yace shugaban kasa an zabeshi ne ya yiwa kasar aiki har zuwa shekarar 2019, kuma abun da ya sa gaba ke nan. Yace lokacin da zai ce zai yi zaben ko ba zai yi ba bai zo ba.Gyaran Najeriya ne a gabansa, inji gwamnan.
  •  A jihar California, wata mota ta abkwa asibitin hakori bayan ta daki jakin babangida sannan ta yi sama ta shige gidan sama. Matukin na cikin yanayin maye a lokacin da hakan ta faru kuma ya rayu.
  •  Gwamnatin Bangladesh ta ce zuwa yanzu ta kirga sama da ‘yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira a sansanonin da ta kafa, wadanda ke kan iyakarta da kasar Myanmar.
  •  Hukumar kula da kwallon kafa ta najeriya NFF, ta tsawaita wa’adin yarjejeniyar mai horar da ‘yan wasan Super Eagles Gernot Rohr.

You may also like