Labarai A Takaice


– Hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa EFCC ta kame tsohon sakataren gwamnatin tarayyar kasar Mista Babachir Lawal.

– A Najeriya Gwamnatin Muhammadu Buhari ta mayar da martani kan wasikar tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo wanda ya bukaci kar shugaban ya nemi tazarce a zaben 2019.

– A jihar Adamawa wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun kai hari a wani kauye inda suka kashe mutune tara da kuma yin awon gaba da wasu kananan yara bakwai.

– Gwamnatin Kamaru ta musanta zargin da tsohon shugaban darikar Katolika na kasar ya yi mata a kan cin zarafin al’ummar bangaren da ke amfani da harshen Ingilishi, wani masani ya tabbatar da cewa ana yin amfani da karfin soji ana musgunawa ‘yan awaren.

– A jiya Laraba ne wasu ‘yan Majalisar Dattijan Amurka suka shirya tunkarar kasar Myanmar kan kisan kare dangi ga wata kabila, inda ‘daya daga cikin ‘yan jam’iyyar Democrat ya zargi shugaban masu rinjaye Mitch McConnell na kin aikata komai kan rikicin Rohingya saboda alakarsa da shugabar kasar, Aung San Suu Kyi.

– A India mahukunta harkokin jiragen saman kasar sun dakatar da lasisin tuka jirgin sama na wadansu matuka jirgin sama guda biyu, bisa laifin dambe da sukayi a cikin jirgi a lokacin da yake sararin samaniya, a farkon shekarar nan ta 2018.

– Masu zanga-zanga na ta kwararowa kan tituna a wasu biranen kasar Switzerland, domin nuna adawarsu ga halartar da shugaban Amurka Donald Trump zai yi taron kolin tattalin arziki na kasashen duniya a Davos cikin wannan makon.

– Shugaban Amurka ya gargadi Turkiyya da ta janye ayyukan sojojinta daga Syria domin kauce ma yiwuwar taho-mu-gama tsakanin sojojin nata da dakarun Amurka da ke kasar.

– Mai horas da kungiyar kwallon kafa na Real Madrid, Zinedine Zidane ya dauki laifin gazawar da ƙungiyarsa ta nuna, inda ta yi rashin nasara a hannun ƙungiyar Leganes a gasar Copa del Rey na Spain.

You may also like