Labarai A Takaice


*Jirgin sama marar matuki na rundunar sojan Najeriya ya harba bom inda ya ragargaza wata katuwar bindiga da ‘yan Boko Haram su ka dasa a dajin Sambisa.*

*Jami’in labarun rundunar sojan saman “AIR VICE MARSHAL” Olatokunbo Adesanya ya baiyana haka.*

*Rundunar dai ta hango wannan katuwar bindiga inda ta tura jirgin ya ragzagaza ta, ta kama da wuta.*

*Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwar shirin daukar sabbin jami’an ‘yan sanda ga matasa ‘yan Najeriya da ke son zama ‘yan sanda.*

*Kakakin rundunar Moshood Jimoh a wata sanarwa ga manema labaru, ya ce za a rubuta shafin yanar gizo na neman shiga rundunar zuwa mako 3 nan gaba.*

*Matasa daga shekaru 18-25 ka iya cike takardar neman shiga ta yanar gizo don gaiyatar su don tantancewa na samun wannan aiki.*

*Cikin ka’idojin akwai samun takardar kammala sakandare da nasara a turanci da lissafi, lafiyar jiki da kyakkyawar dabi’a.*

*Zuwa yanzu dai shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya Farfesa Usman Yusuf bai shiga ofis ba a anguwar Jabi Abuja bayan dawo da shi bakin aiki da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi.*

*Dama tun farko ministan lafiya Isaac Adewole ya dakatar da shit un Yunin bara.*

*Rahoto ya nuna an gaiyaci ministan da kuma mukaddashin shugaban hukumar Attahiru Ibrahim zuwa fadar shugaban Najeriya.*

*A na sa ran kowanne lokaci daga alhamis din nan Usman Yusuf zai koma bakin aiki.*

*Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya jaddada cewa ba zai marawa kowane dan takara a zaben 2019 ba a maimakon haka zai ci gaba da kasancewa cikin iyayen kasa.*

*A makon da ya gabata ne, Obasonjo ya rubutawa Shugaba Buhar wata wasika inda ya caccake shi sannan kuma ya neme shi kan ya jingine batun sake tsayawa takara. Tsohon Shugaban ya kuma kafa wata kungiyar gwagwarmaya wadda aka yi zaton za ta rikide ta koma jam’iyyar siyasa don kawar da gwamnatin Buhari.*

*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci ministan gona Audu Ogbeh ya bude taron majalisar zartarwa da addu’a inda daga nan ya nemi ministan muhalli Jubrin Ibrahim ya bude da addu’ar musulunci amma sai a ka samu baya nan.*

*Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa daga nan sai shugaban ya umurci ministan kwadago Chris Ngige ya yi addu’a.*

*Ganin cewa shi kirista ne kuma ministan gona ya riga ya yi addu’a ta mabiya addinin kirista, sai ya tunatar da shugaban cewa shi kirista ne, duk da haka shugaban ce ya ci gaba da gabatar da addu’a.*

*Shugaban jam’iyyar ANC mai mulki a Afurka ta kudu Cyril Ramaphosa bayan taro da shugaba Jacob Zuma ya ce taron ya yi ma’ana.*

*Yanzu dai manyan shugabannin jam’iyyar za su yi taro daga 17-18 ga watan nan don duba makomar Jacob Zuma da a ke kira gare shi wa imma ya yi murabus don zargin almundahana ko a tsige shi.*

*Masar ta bude mashigar Rafah da ke ba wa Falasdinawa damar kutsowa ko a shiga yankin su daga Masar don samun kayan masarufi da ‘yar sararawar rayuwa.*

*Masar dai kan rufe wannan mashiga don jituwar ta ci gaba da wanzuwa tsakanin ta da gwamnatin Isra’ila. Za a bar mashigar a bude tsawon kwana 3.*

You may also like