Labarai A Takaice


*Kungiyar Izala ta shiga yini na uku a birnin Douala ta jamhuriyar Kamaru. Shugaban Izala sheikh Abdullahi Bala Lau tare da sauran tawagar Maluma sun shiga kasar ne domin gudanar da Da’awar Sunnah*

*Kungiyoyin Ahlussunnah dake fadin kasar kusan duk Sun tare a birnin na Douala domin mubaya’a tare da maraba da kuma rufa baya ga Sheikh Bala Lau tare da sauran Tawagar dake tare da shi*

*Tawagar ta hada da babban sakataren JIBWIS sheikh Kabiru Gombe, Daraktan Agaji Mustapha Imam, Shugaban Alarammomi Abubakar Adam, Shugaban Ayyuka Sheikh Abubakar Giro, Sakataren Alarammomi Nasiru Gwandu, da Dan Autan su shugaban Yada Labarai Ibrahim Baba Suleiman*

*Karamar Ministar Harkokin Waje, Khadija Bukar Abba da Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa, Abdullahi Mohammed sun gabatar wa Shugaba Muhammadu Buhari bayanin irin shirye-shiryen da Najeriya ta yi dangane da aikin Hajjin bana na 2018.*

*Shugaban Hukumar Alhazai Abdullahi Mukhtar ya bayyana cewa Saudiyya ta ware wa maniyyata dubu 95,000 daga Najeriya gurbin shiga kasar domin su gudanar da aikin Hajji.*

*Mukhtar yace an ware kujeru dubu 70,000 ga Hukumar Alhazai, yayin da dubu 20,000 kuma aka ware wa kamfanonin hada-hada masu zaman kan su, wadanda aka fi sani da International, ko kuma jirgin-yawo.*

*Shugaban Naijeriya Muhammadu Buhari ya yi musu alwashin cewa gwamnati za ta bayar da cikakken goyon baya wajen aiwatar da dukkan abin da ya wajaba ga maniyyata, musamman kulawa ta fannin laFiya, tsaro da kayan more rayuwa.*

*Gwmnatin Najeriya na aiki kan jerin sunayen mutanen da za ta kaddamar a matsayin shugabannin hukumomin ta 209 da membobi 1,258 biyo bayan jerin sunayen da a ka fitar da ke dauke da kurakurai har ma da sunayen wadanda su ka riga mu gidan gaskiya.*

*Rahoto ya nuna ofishin sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha na tantance sunayen don kammala aiki tsaf zuwa karshen watan nan.*

*Ministan jirage Hadi Sirika ya kara nanata cewa ba da gangan a ka samu matsala a sunayen tun farko ba, amma gwamnatin na yin duk abu mai yiwuwa don kaddamar da sabbin shugabannin su fara hidima ga al’umma.*

*Bayanin ya nuna akwai ma ma’aikatun da ba a tabo ba a wancan jerin sunayen , don haka za a shigar da su a sabon aikin da a ke yi yanzu.*

*Dattijon siyasar arwacin Najeriya Alh. Dauda Birma ya kaucewa amfani da kafafen labaru wajen fadar abubuwan da ya ke ganin ya dace gwamnatin Buhari ta gyara don samun ribar dimokradiyya.*

*Birma da ke magana bayan kammala taron wani zauren ‘yan siyasar arewacin Najeriya da ke son akalar jagorancin siyasa ya dawo yankin, ya ce shi abokin shugaba Buhari ne, don haka ba zai ba da shawarwarin ta kafafen labaru ba amma zai iya zuwa wajen shugaban su gana.*

*Dauda Birma wanda ya ce yankin arewacin Najeriya na samun koma baya a tasirin siyasa da lamuran tsaro, ya bukaci dukkan al’ummar yankin su ajiyewa bambancin siyasa da muradu waje daya, su yi aiki tare don dawo da martabar yankin mai fadin kasa da yawan jama’a.*

*A karshen makon nan wata mota ta kama da wuta bal-bal a babban titin da ya raba anguwar Wuse 2 da Utako inda a ka rika jin karar fashewar wasu abubuwa a motar da a ke hasashen jarkokin man fetur ne.*

*Gabanin motar ta gama cinyewa kurmus a wajajen minti 15 da faruwar lamarin an ga motar kashe gobara ta garzayo bigiren inda ta kashe wutar. Mutane sun taru don ganin wannan akasi da ya faru lokacin da zirga-zirgar almuru ta fara raguwa.*

*Shugaban hukumar kula da ‘yan sandan Najeriya Mike Okiro yace fiye da jami’an ‘yan sanda 150,000 ke aiki ga masu rike da manyan mukamai da sauran su da hakan ya sanya karfin ‘yan sandan kan tafi ga kula da lafiyar mutane ‘yan kalilan.*

*Okiro ya ce zaka samu mutum ya taba rike minista fiye da shekara 10-15 amma har yanzu ya na yawo da jami’an da hakan bai dace ba.*

*Don haka hukumar ta ce ta na aiki tukuru don janye ‘yan sandan su dawo bakin aiki don kula da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma. Bayanai na nuna jami’an ‘yan sandan na son aiki da tawagar gwamnoni da sauran masu mukami don samun Karin hanyoyin kudi na bulus.*

*Wani jirgin fasinja na kasar Rasha ya fadi dab da babban birnin kasar Mosko inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 71 da ke cikin sa. Jirgin dai ANTONOV-148 ya fadi ne a yankin Ramensky da ke bayan garin Mosko bayan ya tashi daga filin jirgin saman Domodedovo.*

*Fasinjoji 65 ne da ma’aikata 6 a cikin jirgin.*

You may also like