Labarai A Takaice


▪ Gwamnatin Ekiti ta sanya Fulani makiyaya yin rantsuwa kan ba za su zubar da jinin wani dan asalin jihar ba inda aka raba goro a tsakanin wadanda suka yi rants Uwar a bisa ga al’adar makiyayan.

▪ Dillalan Man fetur sun ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 kan ta biya su basussukan Naira Bilyan 650 inda suka nuna cewa bankuna na barazanar kwace masu gidajen mai bisa basussukan da suka karbo a bankunan.

▪Majalisar wakilai ta nemi Shugaban hukumar bayar da Agajin gaggawa ta tarayya, Alhaji Mustafa Maihaja kan ya yi cikakken bayani kan yadda ya sarrafa Naira Bilyan 1.6 da gwamnati ta ware masa don tallafawa ‘yan Nijeriya da aka kwaso daga kasar Libya.

▪Ana ci gaba da ce ce ku ce kan yadda Sakataren Gwamnatin tarayya, Mustafa Boss ya kashe zunzurutun kudade har Naira milyan 65 wajen bude shafin yanar gizo na ofishinsa.

▪Sakamakon wani sauraren ra’ayoyin jama’a da aka gudanar ya nuna cewa Shugaban Amurka, Donald Trump shi ne Shugaba mafi rashin cancanta a jerin shugabannin Amurka.

▪ Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa, ta bayyana cewa kimanin ‘yan Nijeriya 1,306 ne suka mutu a sanadiyyar hadurra daban daban a watanni uku na karshen shekarar da ta gabata a yayin da kuma wasu mutane 7,349 suka samu raunuka sakamakon hadurra.

▪ Jam’iyyar PDP ta koka kan matakin da Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta dauka na gayyato hukumar EFCC kan ta taimaka mata wajen sa ido kan inda jam’iyyun siyasa ke samun kudaden gudanar da harkokinsu.

You may also like