Labarai A Takaice


*Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta rushe wani gida a tsakiyar birnin da bangaren APC mai mulki a jihar da ba ya ga maciji da gwamnan jihar Nasir Elrufai ya kafa a matsayin ofishi.*

*Shugaban hukumar tsara birane ko kula da filaye na jihar Ibrahim Hussaini ya ce hukumar su ta rushe ginin ne don ba a biya ma sa kudin haraji tun shekara ta 2010.*

*Kazalika ginin da ke kan titin SAMBO CLOSE a Unguwar Rimi ya haddasawa makwabtan sa takura ta hanyar samun ‘yan bangar siyasa na karakaina a yankin don haka ya kara zama dalilin rushe ginin.*

*Yanzu dai hukumar ta tsara birane da filaye ta jihar Kaduna ta karbe bigiren filin ginin inda a yanzu za ta shuka furanni a gurbin sa da maida wajen dandalin wasannin shakatawa.*

*Ginin dai mallakar dan majalisar dattawa ne na jihar Kaduna Sanata Sulaiman Hunkuyi da ya kafa ofishin da wani bangare na jam’iyyar APC a jihar inda su ka dakatar da gwamna Nasiru Elrufai da korar wasu mutum 28 daga jam’iyyar.*

*Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci gwamna Nasir Elrufai na jihar Kaduna ya biya diyyar gidan da gwamnatin jihar ta rusa na bangaren jam’iyyar APCmai mulki a jihar ta Kaduna.*

*A bukatar hakan da ta taso daga Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna, ya ce rushe ginin ba ya bisa ka’ida don haka a ba da diyya ko sauyawa mai mallakar ginin wani wajen daban a madadin wanda a ka rusa.*

*Wannan rushe gini na zuwa ne bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin sulhunta ‘yan jam’iyyar sa ta APC karkashin Ahmed Bola Tinubu.*

*Tsohon gwamnan jihar Nassarawa a Najeriya Abdullahi Adamu ya caccaki tsohon shugaban Najeriya Obasanjo kan kiran da ya yi wa shugaba Buhari na ka da ya nemi tazarce a 2019.*

*Adamu ya ce a matsayin sa wanda ya yi gwamna zamani daya da Obasanjo ya ke shugaban Najeriya, ya na da matsayin kalubalantar Obasanjo kan batun shugaba Buhari.*

*Abdullahi Adamu ya ce a matsayin Obasanjo na abokin sa, ya na kira gare shi da ya daina neman rusa duk wani shugaba da ya zo a bayan sa don hakan mummunar dabi’a ce.*

*Rundunar ‘yan sanda a jihar Yobe a Najeriya ta ce ba a samu asarar rai ba a harin da ‘yan Boko Haram su ka kai makarantar sakandaren ‘yan mata ta Dapchi amma sun yi awun gaba da kayan abinci.*

*Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdulmaliki Sumonu ya ce a yanzu dai an samu labarin ‘yan ta’addan sun tafi da wasu mutum 3 maza a yankin karamar hukumar Geidam, amma ba labari na tafiya da ko daliba daya zuwa yanzu daga makarantar.*

*‘Yan ta’addan dai sun yi ta harbi cikin iska don tsorata jama’a a yayin farmakin satar kayan abincin a makarantar.*

*Arangamar da rundunar taron dangi da Saudiyya ke yi wa jagoranci ta kai hare-hare da su ka yi sanadiyyar kashe ‘yan tawayen Houthi 85 a kasar Yaman da kuma jikkata fiye da 100.*

*Kasar Iran dai ke marawa ‘yan Houthi baya da su ka kori zababbiyar gwamnatin Yaman ta Abed Rabbo Mansour Hadi da ya saba da akidar su ta Shi’a.*

*Kwanakin baya ma ‘yan Houthi sun yi wa tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh kisan gilla da nade shi cikin walakanci a wani bargo bayan labarin ya nemi janye yarjejeniyar hulda da su.*

You may also like