Labarai A Takaice


*Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya ce za ta yi wu maso son zama ministoci ne ke son shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi garambawul a gwamantin sa.*

*Shehu a zantawa da shi, ya kara da cewa shugaba Buhari ne ke da ikon dauka ko sauke minista kuma tun da zuwa yanzu bai sauke kowa ba, ba wai hakan na nuna ba zai iya sauke su ba ne, sai dai ko a ce ya na jin dadin aiki da su.*

*Garba Shehu ya shawarci masu ingiza wannan magana su tafi su yi noma maimakon zama su na tsegumin kan sauya ministoci.*

*Haka nan kakakin ya maida martani ga tsoffin manyan jami’an soja da ke nuna rashin gamsuwa ga salon mulkin gwamnatin Buhari, inda ya ce sam ba za su yi nasarar hana sake zaben shugaba Buhari a 2019 ba.*

*Shehu ya ce in ma sun ga dama su zo su tsaya takara da Buhari kuma zai kada su a zabe.*

*Ba mamaki Garba Shehu wanda ya ce zai ja hankalin shugaba Buhari ya nemi tazarce, bai rarrabe a bugun kadanyar da ya yi ba cewa tsohon shugaba Obasanjo da ya fi yada batun kar Buhari ya yi takara, ba shi da hurumin sake takara don ya zama shugaban Najeriya a wa’adi biyu na tsawon shekara 8 daga 1999-2007 baya ga mulkin soja daga 1976-1979.*

*A safiyar Lahadin data gabatarwa Kungiyar Izala ta jihar Borno tayi Taron Yaye matasan yan agaji su 260 a garin Maiduguri fadar jihar Borno*

*Babban daraktan Agaji na kasa, Injiniya Mustapha Imam Sitti da Kansa ya samu halartan taron, kuma yayi bayanai masu inganci ga sabbin yan agajin, kuma ya nuna farin cikinsa ganin yadda yan’agajin suka samu horo da nuna bajinta a yayin basu horon na aikin Agaji domin bada taimakon farko ga majinyaci kafin a kaishi ga Likita. Ya kuma ja hankalin yan agajin da suyi aiki domin Allah, domin samun sakamakon aikin gobe kiyama.*

*Rahotanni na nuna ‘yan bindiga sun ci gaba da ta’addanci a yankin karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna inda su ka bude wuta da kashe mutum 2 da sace wasu mutum 9.*

*Cikin wadanda a ka sace, har da wata sabuwar amarya.*

*Yankin Birnin Gwari ya zama inda zubar da jini ya ta’azzara a yankin jihar Kaduna.*

*Kashe-kashen kan rutsa har da jami’an tsaro hakanan da ma baki masu ratsa yankin don bukatun su na rayuwar yau da kullum.*

*Lauya mai zaman kan sa a Abuja, Yusuf Sallau Mutum Biyu ya ce matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na fadawa shugabannin jam’iyyar sa ta APC gaskiya kan saba ka’ida ga kara mu su wa’addin shekara daya ya yi daidai, amma da tun gabanin Karin ya dace ya hana hakan don kaucewa kawo zullumi a jam’iyyar.*

*Barista Sallau Mutum Biyu wanda ya ke magana a taron karshen wata na kungiyar MA’ABOTA KAFAFEN LABARU a Abuja, ya tuno cewa irin wannan yanayi ya haddasa samun shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekwremadu dan PDP da hakan bai yi wa shugaba Buhari dadi ba kuma ya ke ci gaba da haddasa sabani tsakanin sashen zartarwa da majalisa ma’abota jam’iyya daya.*

*Lauyan ya ce yanzu batun kalubalantar Karin wa’adin na gaban babbar kotun taraiya da ita kuma za ta fassara tanadin doka kan lamarin.*

*Duk da haka lauyan na ganin ya dace jam’iyyar ta yi zama ta sasanta kan ta da kan ta ta hanyar daukar matakin da ya dace.*

*Kotun Kuwait ta yanke hukuncin kisa ga wani mutum dan Lebanon da matar sa ‘yar Sham don kashe mata mai yi mu su aikin gida ‘yar Filifins a gidan da su ka zauna a Kuwait.*

*An gano gawar wacce a ka kashen ne a Firji bayan iyalin sun fice daga Kuwait.*

*Kuwait ta bukaci Lebanon ta mika ma ta mutumin don hukunta shi amma Lebanon ta ki amincewa inda tuni ta damke shi da yi ma sa shari’a a gida.*

*Lamarin ya kawo sabani tsakanin Kuwait da Filifins inda Filifins ta bukaci ‘yan kasar ta su fice daga Kuwait da kuma kin amincewa da takardun neman ‘yan aiki daga kasar zuwa Kuwait.*

You may also like