Labarai A Takaice


– A Najeriya bayan tashe tashen hankula dake aukuwa a jihar Taraba arewa maso gabashin kasar, tawagar sufeta janar na yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ta kai ziyara ta musamman zuwa jihar tare da alkawarin kara yawan ‘yan sanda da kuma samar da jirgin sama mai saukar angulu ga rundunar yan sandan jihar.

– Wasu ‘yan bindiga da ba a gane su ba, sun harbe Magajin Garin wani birni da ke Arewacin Burkina Faso, Hamidou Koundaba har lahira a kusa da iyakar Mali.

– Jiya Talata shugaban kamfanin sada zumunta na Facebook Mr Zukerberg ya bayyana a gaban kwamitocin bincike na majalisun dokokin Amurka akan yadda wani kamfani ya yi amfani da bayanan miliyoyin mutane lokacin zabe.

– A wani taron masana ilimin kimiya a Austria an gano cewa magungunan jinya da ake sayarwa da mutane ke saya ba tare da izinin likitoci ba na gurbatar da ruwan kogi.

– Jiya Talata Fadar shugaban Amurka ta White House ta hakikance akan cewa, shugaban Amurka Donald Trump yana da ikon korar lauya na musaman da aka nada domin binciken alakar dake tsakanin yakin neman zaben shugaba Trump da shishigin da Rasha tayi a zaben shugaban kasar da aka yi.

– Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace tana nazarin al’amura a kasar Sudan bayan shugaban kasar Omar Al Bashir ya bada umarnin nan take a sako dukkan fursunonin siyasa daga gidan yari.

– Yankin Ireland ta Arewa na bikin cika shekaru 20 da yarjejeniyar zaman lafiya mai dimbin tarihi, wanda ya kawo karshen tashin hankalin da aka fuskanta wanda ya lakume rayukan mutane kusan 3,500.

– Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kasa cimma matsayi na bai-daya dangane da matakin da ya kamata a dauka kan kasar Syria a game da zargin amfani da makami mai guba a yakin da ake yi a Syria, a yanzu dai hankula sun karkata zuwa ga kasar Amurka da kawanyenta domin ganin irin matakin da za su dauka kan gwamnatin Bashar Assad.

– Mahukuntan Myanmar sun daure sojoji bakwai a gidan yari sakamakon samun su da hannu a kisan wasu Musulman Rohingya 10 a ranar 2 ga watan Satumban bara a kauyen Inn Din.

You may also like