*Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ba da labarin damke karin mutum 12 da ke da alaka da satar da aka aikata a banki a garin Offa da ke jihar Kwara.*
*Tun farko an damke mutum 8 biyo bayan fashin bankin a ranar 5 ga watan nan. Wasu daga cikin wadanda a ka kama ‘yan garin ne na Offa inda a ciki kuma akwai wani dan jihar Delta.*
*Rundunar ta ce akwai sauran masu hannu a satar da ta ke farauta.*
*Kotun taraiyar Najeriya da ke Lagos ta ki amincewa da bukatar hukumar yaki da cin hanci ta kasar EFCC ta neman karbe zunzurutun kudi fiye da dala miliyan 8 da kuma sama da Naira miliyan 7 da uwargidan tsohon shugaban Najeriya Patience Jonathan ta adana a banki.*
*Alkalin kotun ya ce batun kudin na gaban wasu alkalai biyu don haka ba zai yiwu kotun ta ba da umurnin amshe kudin ba.*
*Tun farko mai taimakawa tsohon shugaban kan lamuran gida Waripamo Dudafa ya ba da shaidar cewa dala miliyan 15.5 da a ka amshewa Patience mallakar ta ne ba na cin hanci da rashawa ba ne.*
*Dudafa ya ce kudin kyautukan da Patience ta samu ne da kuma amanar kudi da a ka ba ta, ta adana.*
*Shugaban rundunar tsaron farar hula na Najeriya CIVIL DEFENCE Muhammad Gana ya ce rundunar ta damke gaggan ‘yan ta’adda na Boko Haram 8 da su ka arce daga Borno.*
*Gana na magana ne a Abuja lokacin da wasu daga daliban makarantar kwarewar manyan jami’an gwamnatin Najeriya da ke Kuru su ka kai ma sa ziyara.*
*Kwamandan rundunar ya ce sun kuma kama wasu masu aikata miyagun laifuka fiye da 100. A nan ya ce rundunar sa ba ta zaman doya da manja da sauran rundunonin tsaro na kasa.*
*Majalisar dattawan Najeriya dai ta dakatar da Omo Agege ne na tsawon kwana 90 bayan rahoton kwamitin ladabtarwa na majalisar da ya ce Agege ya shigar da majalisar da shugaban majalisar dattawan gaban kotu.*
*Tun farko an ba da shawarin a dakatar da Agege tsawon kwanakin majalisa 181 don laifin zaiyana dokar sauya ranakun zabe da cewa an yi hakan ne don hana shugaba Buhari nasarar zaben 2019.*
*A asabar din za a yi taron cika shekaru 4 tun sace matan Chibok a jihar Borno. Yanzu dai saura mata 112 a hannun ‘yan ta’addan.*
*Babban sakataren majlisar dinkin duniya Antonio Guterres ya nuna damuwa kan rahoton amfani da makamai masu guba da gwamnatin Bashar Al’Asad ta yi kan ‘yan turjiya na yankin Douma.*
*Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasashen duniya ke kira ga Rasha ta rungumi tattaunawa wajen warware fitinar Sham ga mara baya da ta ke yi ta hanyar ruwan wuta ta sama ga ‘yan tawaye.*