Labarai A Takaice


– A Najeriya Kwamitin da Shugaban kasa ya kafa don farfado da yankin Arewa maso gabashin kasar ya musanta zarge-zargen cewa ya karkatar da kudaden tallafi da hukumomin agaji ke bayarwa don taimakawa ‘yan gudun hijira.

– A Najeriya an kawo karshen taron manyan hafsoshin sojojin Afirka da rundunar sojan Amurka ta shirya da zummar kawo karshen matsalar tsaro a nahiyar.

– A Najeriya wasu mutum bakwai da rundunar sojan ta nunawa manema labarai akwai amir guda biyu, da ta ce ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram ne da suka mika kansu don kashin kansu a wani gari da ake kira Kumshe dake karamar hukumar Bama a jihar Borno.

– A Najeriya Direbobi sun rufe babbar hanyar da ta hada Adamawa da jihar Taraba sakamakon matsa musu da karbar na goro da jami’an tsaro ke yi.

– Hukumar Majalisar dinkin Duniya dake kula da yan gudun hijira ta bayyana matukar damuwa a kan yadda kasar Kamaru ke ci gaba da tiso keyar yan gudun hijrar Najeriya zuwa gida.

– Shugaban kasar Afrika ta tsakiya Faustin Archange Touadera ya sake jadada aniyar sa ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar ,a dai dai lokacin da wasu yan tsageru dauke da makamai suke kokarin rusa yanayin tsaro a wasu unguwanin babban birnin kasar Bangui.

– Kim Jong Un Shugaban koriya ta arewa a kokarin sa na shirya tattaunawa da hukumomin Koriya ta Kudu a yau asabar ya sanar da dakatar da duk wani gwajin makaman nukiliya,tareda rufe wasu sassan da ake sarrafa ko gudanar da gwajin wadanan makamai.

– A jiya Alhamis ne Rasha ta bukaci Amurka ta biya ta diyya, sakamakon karin kudi harajin ta akan tama da karafa na kasar waje, wanda wannan Rashan ce ta ukku cikin jerin kasashen da ke da tasiri a kungiyar cinikayya ta duniya data bukaci hakan.

– Maaikatar tsaron Amurka tace ga bisa dukkan alamu ba wani sabon yunkuri daga gwamnatin Syria cewa zata sake kai wani sabon harin makami mai guba, hakan koba zai rasa nasaba da harin hadin gwuiwa na ranar Asabar din da Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai ma kasar ba.

You may also like