Labarai A Takaice


Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki da na Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara sun bayyana yiwuwar amince wa da kasafin kudi na 2018 nan da makon gobe bayan wata ganawa da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari a wannan Litinin.

– A Najeriya babban bankin kasar CBN ya ce kasar ta kashe akalla dala biliyan 36, kwatankwacin naira Triliyan 11 wajen shigo da tataccen man fetur daga ketare a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2017.

– A Najeriya shugabannin Fulani da kuma masu sana’ar fawa a jihar Legas sun yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin jihar ke shirin dauka na rushe mayankar shanu ta Agege.

– A jihar Kano bangaren Kwankwasiyya na jam’iyyar APC ya gudanar da nasa zaben shugabanni a jihar Kano daban da wanda uwar jam’iyyar ta shirya.

– Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sake kwato mutum fiye da 1,000 daga hannun mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

– A Zambia Daya daga cikin manyan jami’oi da ke kasar Zambia ta yi kira ga dalibai mata a kan su daina zuwa dakin karatu (laburari) sanye da tufafin da basu dace ba saboda hakan na jan hankalin dalibai maza.

– Yau Talata ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai sanar da matsayinsa na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ko kuma cigaba da zama a cikinta.

– Shugabancin kungiyar Arsenal ya ce nan wani gajeren lokaci zai bayyana sunan sabon mai horar da kungiyar da zai maye gurbin Arsene Wenger, wanda ya rage wasanni biyu ya kammala bankwana da kungiyar.

– Mai horar da kungiyar Liverpool Jurgen Klopp, ya bada tabbacin cewa ya fara yunkurin sayo dan wasan gaba na Barcelona Ousmane Dembele.

You may also like