Labarai A Takaice


– A jiya Juma’a aka yi jana’izar marigayi Shiek Isyaka Rabi’u, shugaban darikar Tijjaniya na Afrika, a masallacinsa da ke goron dutse a jihar Kano a Najeriya.

– Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa babban birnin kasar Abuja da misalin karfe 7 na yammacin jiya bayan shafe kwanaki uku a birnin London wajen duba lafiyarsa.

– Gwamnatin Najeriya ta biya wasu ‘yan kasar 14, ladan naira miliyan 439, sakamakon yadda suka taimakawa gwamnatin, wajen karbo kusan naira biliyan 14 daga masu gujewa biyan kudaden haraji.

– Kungiyar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya kafa don kawar da shugaba Buhari daga mulki ta shiga jam’iyyar adawa ta ADC, da nanata kudirin kawo sabbin jini a harkokin siyasa.

– Asusun tallafawa kana-nan yara na Majalisar Duniya UNICEF, ya ce yara 400,000 suna fuskantar hadarin rasa rayukansu a kasar Congo dalilin tsananin yunwa, muddin ba’a dauki matakai na gagawa ba.

– Ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta dauki matakan shirin ko ta kwana, inda ake sa ido akan shigi da ficen jama’a a akan iyakokin kasar da kuma filayen jiragen sama, bayan samun rahoton sake bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Congo.

– Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani tsari da ke gabanta wanda a karon farko zai kai ga samar da karbabbiyar manufa kan muhalli, bisa yarjejeniyar da kasashen duniya suka kulla a taron rage dumamar yanayi ta Paris ta shekarar 2015.

– Kasashen Jamus da Rasha sun alkawarta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran duk da ficewar Amurka daga cikin wadda ke a matsayin jagora. kasashen biyu a cewar wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar sun cimma hakan ne yayin tattaunawarsu da juna ta wayar tarho.

– Cristiano Ronald ya nemi kungiyarsa ta Real Madrid ta kara masa albashin da yake karba zuwa euro 500,000 a mako daya.

You may also like