Labarai A Takaice


– A Najeriya Kungiyar lauyoyin kasar ta yi taro a Kano inda ta tabo abubuwan dake damun kasar da yadda za’a magancesu domin kasar ta ci gaba. Mahalarta taron dai sun fito ne daga jihohin kasar 36 da kuma Abuja kuma shugaban kungiyar na kasa Abubakar Balarabe Mahmud, SAN, shi ne jagoran taron.

– Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce ta kafa kwamitocin karban korafe-korafe a duk jihohin kasar da za su warware matsalolin da suka taso sakamakon zabukan shugabannin jam’iyyar da aka yi a mazabun kasar.

– Shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimpianina, ya amince da wata sabuwar dokar zaben kasar, da ta dage haramcin da a baya ya hau kan madugun ‘yan adawa kuma tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana na sake tsayawa takara

– A kasar China, yan Sanda sun hana jakadun kasashen Faransa, Jamus , kungiyar tarrayar Turai da wasu kasashe biyu kaiwa matar marigayi Liu Xiaoboo mutumen nan da ya lashe kyautar Nobel na shekara ta 2010 ziyara a gidan ta.

– A Lebanon wasu mukaraban Firaministan kasar Saad Hariri sun yi murabis yan lokuta bayan fitar da sakamakon zaben yan Majalisun kasar wanda ga baki daya Firaministan ya kasa samun rijaye.

– Wani sabon ibtila’in zabtarewar laka sakamakon kakkarfan ruwan sama hade da iska a India ya hallaka akalla mutane 40 a jiya lahadi.

– Yau kasar Amurka ke bude ofishin Jakadancinta a birnin Kudus duk da fargabar da kasashen duniya ke yi na cewar matakin ka iya dakushe shirin zaman lafiya tsakanin Israila da Falasdinu.

– Wasu ‘yan kunar bakin wake 4 akan babura sun tada bam a shalkwatan ‘yan Sandan birnin Surabaya da ke kasar Indonesia, in da suka raunana jami’ai akalla 10, bayan sun hallaka kansu.

– Korea ta Arewa ba za ta watsar da daukacin makamanta na nukiliya ba kamar yadda wani tsohon mataimakin jakadan kasar a Birtaniya, Thae Yong-ho ya yi hasashe a wata zantawa da manema labarai.

– Bayanai sun ce mataimakin mai horar da kungiyar Manchester City, Mikel Arteta na kan gaba, a tsakanin takwarorinsa da ake fatan ganin sun karbi ragamar horar da kungiyar Arsenal.

– Barcelona ta gaza kafa tarihin kammala kakar gasar La Liga ta bana ba tare da an doke ta ko sau daya ba, bayan Levante ta zazzaga mata kwallaye 5-4 a karawar da suka yi a jiya, lamarin da ya bakanta ran magoya bayan kungiyar a sassan duniya.

You may also like