– A Najeriya Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Addin Islama a kasar, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bukaci Musulman da ke sassan kasar da su nemi jinjirin watan Ramadan a ranar Laraba mai zuwa.
– A cigaba da ziyarar kwana biyu da ya keyi a Jihar Jigawa Shugaba Buhari ya bude cibiyar samar da ruwa a Dutse wadda ta kara lita miliyan tara bisa hudun da ake samu da kowace rana, ke nan yanzu kullum Dutse da kewaye zasu samu lita miliyan 13.
– Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce yaki da cin hanci da rashawa ba zai samu cin nasara ba sai an dawo da kudaden Afirka da aka sace a ka boye a bankunan kasashen waje.
– A taron hukumomin dake yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka renon Ingila, da aka yi a Abuja, mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce kasashen na hasarar dalar Amurka biliyan 50 a shekara sanadiyar almundahana.
– A Najeriya wani dandazon mabiya Shi’a da ke zanga-zanga kan bukatar sakin jagoransu Ibrahim Yakubu Zakzaky da gwamnatin kasar ke ci gaba da tsare da shi kusan shekaru 3, sun farwa jami’an ‘yansandan da ke Sakateriyar gwamnatin Tarayya a Abuja babban birnin kasar.
– Gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta yi bikin kona bindigogi kusan 6,000 da ta karbe daga hannu ‘yan bindiga a karkashin shirinta na afuwa.
– Akalla Falasdinawa 52 Isra’ila ta hallaka ciki har da kananan yara 8 da shekarunsu bai gaza 16 ba, baya ga jikkata karin wasu fiye da dubu 2 a boren da Falasdinawan ke ci gaba da yi kan mayar da Qudus babban birnin Isra’ila.
– Kasashen duniya na ci gaba da Allah-wadai da Isra’ila kan kisan da sojojinta suka yi wa Falasdinawa 59 da ke zanga-zangar lumana ba tare da makami ba a Gaza, lokacin da Amurka ke bude sabon ofishin Jakadancinta a birnin Kudus.
– Mai horar da tawagar kwallon kafar Najeriya Gernot Rohr ya fitar da jerin sunaye na wucen gadi na ‘yan wasa 30 da za su wakilcin kasar a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci nan da kwanaki 30 masu zuwa.