Labarai A Takaice


– Rundunar sojin Najeriya ta fitar da rahoton kwamitin da ta kafa na bincikar zargin da tsohon hafsan sojin kasar Lafatanar janar Theophilus Danjuma ya yi, na cewa, jami’an sojin kasar sun hada kai da makiyaya wajen hallaka mutane da dama na wasu kabilu yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a Jihar Taraba.

– Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Al. ta gudanar da wani taron gaggawa a jihar Kaduna, inda ta cimma matsayar ci gaba da zama akan bakanta na kalubalantar dokar haramta kiwo da gwamnatin jihar Benue ta kafa.

– An zabi mukkadashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu, a matsayin sabon shugaban hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na ilahirin kasashen kungiyar Commonwealth da ke nahiyar Afrika.

– Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar dakile yunkurin wasu ‘yan kunar bakin wake mata, da suka yi kokarin kaiwa sojoji hari a Kawuri da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

– Wasu mahara kan babura dauke da mugan makamai sun kashe Fulani 17 a kauyen Aghay dake Inates yankin Tillabery a Jamhuriyar Nijar da kan iyaka da kasar Mali.

– Hadin gwiwar rudunonin tsaron kasashen Ghana, da Togo da Benin da kuma Burkina Faso sun yi nasarar kamo mutane 202 a kan iyakokin kasashen su daga ranar 15 zuwa 18 ga wannan watan da muke cikin sa., wadanda ake zargi da aikata laifuffuka daban daban.

-Jam’iyyun adawa a Burundi sun ce ba zasu amince da sakamakon zaben raba gardamar da ya gudana ba akan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, wanda zai baiwa shugaba Pierre Nkrunziza damar kaiwa shekara ta 2034 akan mulki.

– Shugabannin kasashen Musulmi sun bukaci kafa rundunar hadin gwiwa ta dakarun kasa da kasa, domin baiwa falasdinawa tsaro, bayanda jami’an tsaron Isra’ila suka hallaka akalla falasdinawan 60 a yankin Zirin Gaza cikin wannan makon.

– A jiya asabar aka gudanar bikin daurin auren Yarima Harry na Birtaniya da Meghan Markle a Fadar Windsor inda dubban baki daga sassan duniya suka halarta. Fadar Windsor dake da nisan kilomita kusan 30 da birnin London tayi cikar kwari da daruruwan baki da kuma mutanen gari da suka yi dafifi a titunan da ma’auaranta biyu suka kewaya a keken doki.

– Jami’an Diflomasiya daga nahiyar turai, China da kuma Rasha sun fara tattaunawa kan samar da wata yarjejeniya, wadda a cikinta zasu mikawa Iran taimakon kudade domin ta dakatar da shirinta na kera manyan makamai masu linzami, hadi da rage tasirinta a al’amuran diflomasiya da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

– Chelsea ta lashe kofin kalu-bale na Ingila bayan da ta doke Manchester United da ci 1 mai ban haushi.

– Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho ya ce Chelsea bata cancanci nasarar lashe kofin gasar FA da ta yi ba.

– Mai tsaron raga na Juventus Gianluigi Buffon ya samu kyautuka da karramawar magoya bayan kungiyar, bayan da ya kawo karshen wasa a cikinta a fafatawar da suka yi da Verona.

You may also like