Labarai A Takaice


– Babbar kotun Najeriya da ke birnin Abuja ta yanke hukuncin dauri a gidan yari kan tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame har tsawon shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba.

– Kungiyar tsaffin ‘yan jam’iyyar PDP da a yanzu ke APC mai mulkin Najeriya, ta musanta mikawa gwamnati bukatar dakatar da shara’ar da ake yi wa shugaban majalisar dattijan kasar Sanata Bukola Saraki akan kin bayyana wasu kadarorinsa.

– A Najeriya jam’iyyar APC mai mulkin kasar na fuskantar sa in sa a cikin gida, kasa da watanni 9 kafin gudanar da zaben kasar a shekarar 2019, ganin yadda wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka fito daga PDP ke kukan ba a yi musu adalci.

– Kungiyar Amnesty International na zargin jami’an tsaron Najeriya da yi wa mata fyade a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno ta Najeriya.

– Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa akwai karancin yekuwar da ake yi wa jama’a kan illar da ke tattare da sigari wajen haifar da cuta ga zuciyar dan adam.

– Wata kungiya mai kula da matsugunnan yahudawa ta ce Isra’ila ta amince da gina karin muhallan yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna 1,958 a wani sabon wuri da ke a yankin zirin Gaza.

– A karon farko cikin shekaru biyu ‘yan uwan juna Serena Willimas da Venus Williams sun yi nasarar kai wa ga zagaye na biyu a gasar tennis ta French Open ko Roland Garros da ke gudana a Faransa ajin ‘yan wasa biyu-biyu.

– Lionel Messi ya zarta tsohon gwarzon dan kwallon duniya Ronaldo Nazario na Brazil wajen zama daya daga cikin ‘ya wasan da suka fi yawan zura kwallaye a tarihin yankin Kudancin Amurka.

– Mai horar da Real Madrid Zinadine Zidane, yau Alhamis ya sanar da matakinsa na rabuwa da kungiyar, kwanaki kalilan bayanda ya jagorance ta sake lashe kofin gasar Zakarun Turai karo na 3 a jere.

You may also like