Labari Mai Dadi Ga Najeriya Yayin Da Farashin Gangar Man Fetur Ya Kai $57Farashin gangar man fetur yakai dalar Amurika $57 bayan da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta cire Najeriya da kuma kasar Libya  daga jerin kasashen da za su rage man da suke hakowa a kowace rana.

 Kasashe mambobin kungiyar dama wadanda ba mambobin kungiyar ba tun farkon watan Disambar shekarar 2016  suka  amince su rage man fetur din da suke hakowa, a kokarin da suke na rage yawa danyen  man a kasuwar duniya wanda ya jawo faduwar  kudin kowacce gangar mai daya zuwa $29 a farkon shekarar 2016.

Har zuwa yammacin ranar Litinin,gangar danyen bakin mai da ake kira Brent ana sai da ita kan $57.57 karin $1.15 akan yadda aka siyar da ita a ranar  Juma’a.

 A taron ministocin man fetur din kasashe mambobin kungiyar dama wadanda ba mambobin kungiyar ba da aka gudanar a birnin Vienna  na kasar Austria, sun amince da a cigaba da aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla tunda farko. 

Wasu kasashe mambobin kungiyar sun bayyana damuwarsu kan kari da aka samu na yawan man da Najeriya da kuma kasar Libya suke fitarwa.

Emmanuel Kachiku karamin ministan man fetur na Najeriya, wanda ya jagoranci tawagar kasar zuwa wurin taron  yayi nuni da cewa duk da ana samun nasara a kokarin da kasar take na kara yawan man da take hakowa tun daga watan Oktoban shekarar data gabata har yanzu Najeriya bata gama fita daga matsalar da take fama da ita ba.  

You may also like