
An sayar da Hadizatou Mani ga wani mutum karkashin koyarwar wahaya a Jamhuriyar Nijar
Daga Caroline Mwangi da Muktar Sadu Alize
An sayar da Hadizatou Mani-Karou ga wani basaraken kauye lokacin tana da shekaru 12, ta kuma zamo mace ta biyar a wurin mutumin a wani tsari da ake kira Wahaya ko ”mace ta biyar”, yanayi ne mai matukar tayar da hankali.
“Ba ni da wani ‘yanci; babu hutu, babu abinci, babu kwanciyar hankali,” in ji matar a shirin BBC na Mata 100, a lokacin tana gidansu da ke kudancin jamhuriyar Nijar.
Tsarin Wahaya ba shi da bambanci da bauta a yankinsu, tsari ne da attajiri ke sayen mace domin ta yi aikin bauta, da gamsar da sha’awarsu ta jima’i kan kudin da bai wuce 100,000.
Suna kasancewa macen aure ta biyar, duk da addinin musulunci ya haramta auren mace fiye da hudu.
A shekarar 1996 aka sayar da Hadizatou, ta kuma shekara 11 tana aikin bauta. Sai dai tashin hankali da ukubar da ta shiga bai tsaya nan ba.
Bayan samun ‘yanci a shekarar 2005, ta yi aure da wanda ta zabawa kanta, amma sai tsohon mijinta ya maka ta a kotu kan ta yi aure kan aurensa, an kuma yanke wa Hadizatou hukuncin zaman kaso duk da tana da juna biyu.
Amma bayan sama da shekara 10, ta yi nasara a shari’ar da ta daukaka. Wannan babbar nasara ce ga al’ummar Jamhuriyar Nijar, inda ba a dauki bautar dan adam a bakin komai ba.
A yanzu Mani na zaune a garin Zongo Kagagi da ke kudancin jihar Tawa, tana wayar da kan mata kan sanin ‘yancinsu da illar bauta da yadda za su kubutar da kansu daga wannan hali.
Tana daya daga cikin matan da BBC ta yi hira da su a shirin Mata 100 da suka kawo sauyi a duniya. A wannan shekarar, BBC tana jin dadin yadda shirin ya kawo sauyi shekaru 10 da kaddamar da shi.
Batun Mani ya kasance abin yin duba a tsanaki da har ya kai ga sauya wata doka a kasarta.
Amma duk da hukuncin da kotu ya yanke, Mis Mani ba ta tsayar da gangamin da take yi na wayar da kan mata ba, saboda har yanzu sama da mutane 130,000 na ci gaba da fuskantar bauta da tsananin wahala a Jamhuriyar Nijar, kamar yadda kididdigar hukumar yaki da bauta ta Global Slavery ta bayyana.
Hadizatou Mani na zaune da iyalanta a kudancin jamhuriyar Nijar
Karin matar aure
“Macen aure ta biyar” ba su da bambanci da bayi ga attajiran da ke yankin, kuma sukan yi kyautar su ga wasu a wani mataki da ake kira Sadaka.
Da tsarin Wahaya da Sadaka abu daya ne, kuma kunci daya suke fuskanta wato safararsu domin gamsuwar jima’a da bauta.
Akan yi wa mace ta biyar kallon kwarkwara ga wanda suke karkashinsa, yana da wasu matan hudu da addinin Musulunci ya ba shi damar aura tare da tara zuri’a.
Suna shiga tashin hankalin da ke fitar da su daga hayyaci, da tunani, da kunci da tarin bakin ciki ga kuma ukubar jima’in da ba su da muradin yi da cin zarafi har da lakada musu duka idan ba su yi biyayya ba. A kan hana su abinci, a tilasta musu aikin wahala na gida daga shara, wanke-wanke da aikin gona ko kiwo da sauransu.
Wannan ita ce rayuwar da Hadizatou Mani-Koroau ta fuskanta lokacin da aka sayo ta daga Nijar tare da tsallaka iyakar Najeriya da ita zuwa Nijar.
Ta ce attajirin mutumin ya zuba makudan kudade wajen siyasanta da kuma wasu karin matan bakwai.
An yi cinikin ta ba tare da iyayenta na wurin ba ko sanin nawa aka biya ba.
Bakar azabar da ake gana mata ta janyo tserewarta gida amma duk lokacin da ta je sai a taso keyarsa ta a sake mayar da ita Nijar, kuma hukuncin da take fuskanta ya fi na baya tsanani.
”Yakan shaida min ni baiwarsa ce, sai yadda ya ga damar yi da ni tun da kudi ya sanya ya sayo ni kamar akuya,” in ji Mani. Ta kuma ce ya yi mata fyade ba adadi tare da tilasta ma ta haihuwar ‘ya’yan da su ma bayi ne a gare shi.
Asalin hoton, Getty Images
Ms Mani (dauke da yarinya) lokacin da ta bayyana a kotu da ke Yamai a shekarar 2008
An soma amfani da tsarin Wahaya daruruwan shekaru da suka wuce, kuma har yanzu ana ci gaba da bin tsarin ko a boye ko kuma bayyane.
A karni na 20 ne Turan mulkin mallaka na Faransa suka haramta yin shi, amma sai mutane musamman attajirai sn yi kunnen uwar shegu da batun tare da yin abin da suka ga dama.
A shekarar 1960 karkashin wata sabuwar dokar kundin tsarin mulkin Nijar, an sake haramt aikin bauta da sayan bayi, sai dai rubutun a takarda kadai ya tsaya, domin an ci gaba yi ba tare da wata fargaba ba.
A hankali kasar ta taka wani mataki shekrar 2003, inda aka haramta wahaya baki daya tare da ayyana aikatawa da mummunan laifi da mutum ka iya fuskantar zaman kason shekaru da dama.
Wannan hukuncin ne, ya bai wa Mis Mani shakar iskar ‘yanci, a shekarar 2005 ta samu ‘yancin barin gidan ukuba tare da ‘ya’yanta guda biyu.
Amma bayan shekara guda, da ta yunkuro domin akara aure, sai mijin bautarta ya maka ta a kotu kan zargin aure kan na shi auren, ya kafe har a lokacin ya
‘Da’ira mai abin kunya’
An samu Ms Mani da laifin yin aure kan aure, aka kuma yanke mata hukuncin zaman kason watanni 6, amma daga bisani shari’a ta sauya a shekarar 2019.
Daga nan sai ta shigar da gwamnatin jamhuriyar Nijar kara gaban kotun Ecowas, lmarin da ya kai ta d yin ggarumar nasara.
Alkalai sun ce jamhuriyar Nijar ta take dokokin da aka kafa na haramta bauta, ta hanyar kin hukunta tsohon mijin Mani da ya azabtar da ita, sun kuma gaza ba ta kariyar da ta ke bukata.
A shekarar 2009 ne, Gwamnatin Nijar ta boiya ta diyyar dala 20,000 kwatankwacin CFA 10,000,000.
Hukumar yaki da kangin bauta ta Nijar ce ta dauki nauyin tsayawa Mis Mani by Niger’s anti-slavery organisation Timidria da wata kungiya mai zaman kan ta ta Birtaniya mai yaki da bauta a duniya su ne suka taimaka ma ta kai ga wannan nasara.
Shugaban hukumar Timidria Association president Ali Bouzou, ya ce har yanzu ba a daina muguwar dabi’ar bautar da mutane da sayo su ba musammana ayankunanan Konni, Madaoua-Bouza da Illela, yanyi ne da muke kira yankuna masu ban takaici da kunya,” in ji shi.
Asalin hoton, Timidria
A shekarar 2009, aka bai wa Ms Mani lambar yabo ta matan da suke da kwarin gwiwa. Sun dauki wannan hoto tare da maidakin shugaban Amirka Michelle Obama da tsohuwar matar shugaban kasa Hillary Clinton.
An fara daukar matakai a jamhuriyar Nijar karkahin sabuwar dokar.
Tsakanin shekarun 2003 zuwa farkon 2022, an kai korafin bautar da mutane sau 114, kamar yadda Mista Bouzou ya bayyana, kuma an yanke hukunci kan mutum 55 gaban shari’a, yayin da aka zartar da hukunci kan mutum shida amma hudu daga ciki an yi watsi da su daga baya.
Kwararru da masu rajin kare hakkin dan adam da bauta na cewa kamata ya yi a yanke wa wadanda ka samu da sayen bayi da azabtar da su hukunci tsakanin shekara 10 zuwa 20 a gidan kaso.
Ana kuma kiraye-kirayen adauki tsauraran matakai akan iyakokin, wanda yawanci ta nan ake safarar mutanen da jefa su cikin mawuyacin hali, in ji Mista Bouzou.
Sai kuma wani kokarin da ake ganin malman addinin musulunci ya kamta su daukai na bayyana karara haramcin da ke cikin tsrin wahaya da sadaka.
Sai dai har yanzu cinikin bayi da azabtar da su na ci gaba da zama babbar matsala a duniya.
Farfesa Dawood Chirwa shi ne shugaban sashen Shari’a a jami’ar Cape Town ta Afirka ta Kudu, kuma jagaba a asusun Majalisar Dinkin Duniya da ke daukar mataki kan bauta, ya ce lmarin na kara gaba a kowacce rana, musamman lokacin da cutar korona ta barke, da kuma yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine.
Ya ambato wani rahoto da hukumar kwadago da hukumar da ke sa ido kan kaura da ke aiki karkshin Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2022, cewa akwai mutane kusan miliyan 50 da suke rayuwa karkashin tsarin bauta, kuma sama da miliyan bakwai a nahiyar Afirka suke.
“Yaki da aikin bauta ya zama abu mai matukar wuya a nahiyar Afirka, babu wata kwakkwarar doka da za ta hukunta mutanen da aka samu da aikata laifin, duk da cewa dokokin kasa da kasa na yaki da bauta sun tanadi hakan,” in ji Farfesa Chirwa.
A yau, Hadizatou Mani na cike d farin ciki da walwala ta kuma kuma jin dadin zama da sabon mijin ta, ta na ‘ya’ya bakwai wadanda ke tsakanin shekaru 1 zuwa 21.
Ta taimaka wa mata bila adadin, ciki har da ‘yar uwarta, domin kubuta daga kangin bauta da smun ingantacciyar rayuwa. ” Na koyawa mata yadda za su kare kan su da kwatar ‘yancinsu, har gaban shari’a,” in ji Hadizatou.
“Ban taba yin nadamar abubuwan da suka faru dani ba…. Ba laifina ba ne, haka kaddarata take, kuma na yi kokarin sauya rayuwata da zamewa mata katanga ko tsanin kaucewa matsalolin da suka hada da na wahaya da sadaka.”