Laberiya na bukatar malaman makaranta 6000 daga Najeriya – George Weah


Shugaban kasar Laberiya, George Weah ya ce kasarsa na bukatar malaman makaranta akalla 6000 daga Najeriya.

Weah ya bayyana haka a ranar Litinin lokacin da ya ziyarci shugaban kasa, Muhammad Buhari, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya bayyana cewa tattalin arzikin Laberiya  na cikin wani mawuyacin hali, Weah ya ce kasarsa na bukatar masu zuba jari daga Najeriya.

Shugaban na Laberiya ya dora laifin matsalar tattalin arzikin da kasarsa ke fama da ita kan faduwar farashin kayayyakin da kasar ke fitarwa kasashen waje da kuma musayar kudin kasashen waje.

“Farashin abubuwa biyu da muka fi fitarwa wato roba da kuma karfe na cigaba da faduwa a kasuwar duniya haka ya kawo raguwar kudaden musaya da muke samu daga wandannan abubuwa ana amfani da kudin yawanci wajen shigo da kayan abinci da sauran abubuwan amfani, hakan ya sa aka samu wagegen gibin kasuwanci, rashin aikin yi tsakanin matasa ya yi yawa fiye da ko yaushe kuma farashi kayan amfanin yau da kullum sai karuwa ya ke,”ya ce.

Weah ya kara da cewa karakashin shirin yarjejeniyar musayar malamai da Najeriya , kasarsa na bukatar karin malamai 6000 domin cike gibin karancin ingantattun  malamai a fannin ilimin kasar 

You may also like