Hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu matukar raguwar cuta mashaƙo, amma cutar ta sake karuwa a baya-bayan nan.
Cutar ta fi tsanani a kan yara da manyan da basu da allurar rigakafinta, domin yawan yin rigakafin ne ya sa cutar ta ragu sosai a tsakanin shekarun 1980 zuwa 2021, a duniya.
Sai dai a shekarar 2019, cutar mashako da ake kira Diphtheria a likitance ta kama sama da mutane 20, 000.
Najerya, kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afrika, ta fuskanci barkewar tun a watan Oktobar shekarar 2022.
Kuma tun bayan bullar cutar zuwa watan Janairun 2023, muane 38 ne aka tabatar sun mutu a sanadiyyar cutar, a kasar.
Lamarin da likitoci ke dangantawa da rashin yin rigakafinta, wanda hakan ne kadai maganin cutar kawo yanzu.