Lafiya Zinariya: Bayanai kan magungunan cuar kansa



Bayanan sauti

Danna hoton sama ku saurari shirin:

Daya daga cikin manyan hanyoyin da ake maganin ciwon daji shi ne halin wasu magunguna da ake kira chemotherapy, amma dumbin mutane musamman a wasu kasashen yammacin Afrika suna fargabar bin wannan hanya.

Wasu daga cikin dalilin da ke sa mutane dari-dari da magungunan su ne illolin da ke tattare da su ta fannin kiwon lafiya.

A Najeriya kasar da ta fi kowa yawan al’umma a nahiyar Afrika, wadannan magunguna na da tsadar gaske, bugu da kari kuma ba a ko’ina ake samunsu ba.

Wani hadarin da masu cutar sankara ke fuskanta a kasar shi ne idan aka yi rashin dace wajen zuwa ga likitocin da basu da kwarewar bayar da magungunan.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like