Latsa lasifikar da ke sama domin sauraron shirin
A nahiyar Afirka ana haihuwar yara da ciwon dundumi, cutar da ke janyo makanta a tsakanin manya idan ba a dauki matakan da suka dace a kan lokaci ba. In ji likitoci
Yara kan yi gadon wannan cuta daga iyaye ko dangi kuma an iya haihuwarsu da shi.
Wasu daga ciki alamomin da ake gane yara na ɗauke da wannan cuta ita ce idanuwansu za suna ƙara girma kuma suna yawan zubar da hawaye.
Sai dai masana a fannin kiwon lafiya sun shawarci iyayen da suka fahimci hakan su kai yaransu asibiti domin a tabbatar da hakan maimakon ƙoƙarin yin magani da kansu.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce kimanin mutane 7.7 miliyan ne ke fama da wannan cuta ta dundumi a faɗin duniya.
Cutar dundumi nau’oi uku ne akwai na yara da wanda ya fi yawa a nahiyar Afirka wanda gani ke fara raguwa ta gefen ido saboda nauyin da ruwan ido ya janyo wa idon.
Sai na ukunsu wanda shi kuma ya shafi halitta da yasa gefen idon bai buɗe da kyau ba, wanda an fi samunsu a fararen fata.
An ware ranar 12 ga watan Maris na kowace shekara, a matsayin ranar cutar dundumi ta duniya
Inda daga wannan ranar ne ake kwashe tsawon mako guda ana wayar da kan jama’a, domin kawo ƙarshen makantar da cutar ke janyowa.
Sannan ana fɗakar da mutane kan muhimmancin zuwa a duba idonsu a kai-a-kai don gano cutar.