Laftanal Kamal Muhammad Abu Ali,  Wanene shi kuma Wacce Jarumta Ya Nuna? 


Labarin rasuwar kwamandan rundunar sojin Nijeriya ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali, shi ne kusan batun da ya fi kowanne jan hankalin ma’abota shafukan sada zumunta a Nijeriya a ranakun karshen mako.
Laftanal Kanal Abu Ali yana cikin sojoji biyar da suka rasa rayukansu a daren Juma’a, yayin bata kashi da mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai hari kan wani barikin soji dake Mallam Fatori a jihar Borno.
Rundunar sojojin Nijeriyar ta sha bayyana dakarunta da su ke rasa rayukansu a rikicin Boko Haram, a matsayin jarumai, wadanda suka sadaukar da rayukansu don kare rayukan sauran jama’ar kasar.
Sai dai a wurin hukumomin sojin Nijeriyar, jarumtar Laftanar Kanar Muhammad Abu-Ali ta daban ce. Hakan ne ma ya sa ya samu karin girma na daban a cikin yakin da ake yi da Boko Haram.
A watan Satumban 2015 a Gamboru Ngala, babban hafsan sojin kasa na Nijeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai ya yi masa karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman.

Wace irin jarumta ya nuna?
A cikin sanarwar sojin kasar wacce ta tabbatar da kashe Laftanar Kanar Abu-Ali, kakakin rundunar sojin kasa ta Nijeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka ya bayyana shi a matsayin sojan da ya nuna jarumta ta daban.
Hakan ne a cewar shi, ya sa aka yi masa karin girma tun kafin ya cika shekarun samun karin girman.
Kanal Kukasheka ya kara da cewa idan ana neman jarumin soja, to idan aka samu Laftanal Kanal Abu Ali, babu sauran magana kuma:

Wanene Laftanal Kanal Muh’d Abu Ali?
Masu sharhi da marubuta da dama a Nijeriyar sun ce mariganyi Laftanar Kanar Abu-Ali, ya yi suna ne a yakin da dakarun kasar ke ci gaba da yi na kawar da kungiyar Boko Haram.
A wani rubutu na girmamawa ga mamacin, Hamza Idris, tsohon ma’aikacin jaridar Daily Trust a arewa maso gabashin Najeriya, ya bayyana shi a matsayin mutun mai zuciya irin ta zaki, sarkin daji wanda ba ya gudu, ba ya ja da baya har zuwa lokacin da rayuwarshi ta kare.

A cewar Idris, mutanen jihar Borno, wadanda su ne suka fi shan wahalar rikicin Boko Haram, su ne za su fi kowa sanin wanene Laftanar Kanar Abu-Ali, saboda a cewarshi, Laftanar Kanar Abu-Ali, ya na gaba-gaba a cikin sojojin da suka sarrafa manyan makaman da aka girke a arewa maso gabashin Najeriya domin yaki da Boko Haram.
Tun a watan Yunin wannan shekara, lokacin da ba wanda ya kawo cewa ta Allah za ta faru da Laftanar Kanar Abu-Ali a wannan lokaci, Editan jaridar TheCable, wacce ake wallafa wa a intanet, Fisayo Soyombo ya yi rubutu na jinjinawa jarumtar sojan.
Soyombo ya ce kamar yadda rahotanni suka nuna, jaruntar da Laftanar Kanar Abu-Ali ya nuna wajen sarrafa tankokin yaki, ita ta taimaka sojoji suka kwato garin Baga da Gamboru-Ngala daga hannun kungiyar Boko Haram.
Wasu sojoji da suka yi aiki a karkashinsa, sun shaida wa BBC cewa samun jagora irin Laftanar Kanar Abu-Ali ya na da wuya, domin shi mutun ne mai karfafa gwiwar na kasa da shi, da kula da bukatunsu, da shiga gaba a duk inda aka dosa.
Marigayin dan asalin jihar Kogi ne, kuma da ne ga basaraken masarautar Nge, Birgediya Janar Abu Ali mai ritaya.

You may also like