Lagarde za ta fuskanci shari’a


Kotu a Faransa ta ce shugabar IMF Christine Lagarde za ta gurfana gaban kotu kan biyan attajirin nan Bernard Tapie tsabar kudi euro miliyan 400 lokacin da ta ke ministar kudi.

 

 

largarde

A hukuncin da kotun ta yanke dai, ta ce Lagarde ta yi sakaci wajen amincewa da biyan wadannan kudade da suka danganci shari’a da aka yi, kuma hakan ya haifar tada jijiyar wuya don haka dole ne ta fuskanci hukunci kan wannan sakaci.

Shugabar ta IMF dai ta musanta yin ba daidai ba dangane da wannan batu, hakan ne ma ya sanya ta tun da fari ta nemi wata kotu da ta dakatar da batun shari’ar. Ya zuwa yanzu dai Lagarde din ba ta kai ga maida martani game da wannan matsayar da kotun ta dauka ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like