Lagos –  An gwabza mummunan fada tsakanin Hausawa da Fulani. 


Jihar Lagos a arewacin Nigeria an gwabza mummunan fada tsakanin Fulani da Hausawa a babbar mayankar dabobbi dake Agege.
Ni ganau ne ba jiyau ba,  naje kallon yanayin yadda akw gudanar da al’amura a wajen don gabarowar Sallah,  in da naji hatsaniya ta fara faruwa,  saga bisani aka fara dauko gariyo da adduna, Da kyar Allah ya tseratar danindaga wajen, bayan abu ya lafa,  na samu labarin am samu asarar rayuka a wajen wanda kuma ba abin mamaki bane  bisa la’akari da irin makaman da aka fito dasu,  inji daya daga cikin Ma’aikatan mu na Arewa24News. 

Amma rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta musanta batun asarar rayuka.’Yan sanda sun ce, fadan ya samo asali ne bayan wani Bafulatani ya bugi wata budurwa Bahaushiya, lamarin da Hausawa ba su ji dadinsa ba. 

Wannan ta sa an gwabza fada tsakanin Hausawan da Fulani.

You may also like