Gwamnan jihar Plateau Simon Lalong yace sai da ya shawarci takwaransa na jihar Benue, Samuel Ortom kan aiwatar da dokar hana kiwon shanu a fili.
Lalong ya fadi haka lokacin da yake tattaunawa da manema labarai dake fadar shugaban kasa a yau bayan wata ganawa da yayi da shugaban kasa Muhammad Buhari.
A yan kwanakin nan an rawaito cewa fulani makiyaya sun kashe mutane da dama a jihar Benue.
A cewar Lalong ba fulani ne kaɗai ba, ke kiwon dabbobi.
Gwamnan yace jihar Filato na cin gajiyar zaman lafiyar da aka samu ne a jihar saboda gwamnati ta haɗa kai da kowa, fulani da manoma baki ɗaya.
Lalong ya kuma ce ya gamsu da shirin gwamnatin tarayya na samar da wurin kiwo a jihar a matsayin wata hanya ta kawo karshen rikicin dake faruwa tsakanin fulani makiyaya da manoma dake yawan faruwa.