Lalong ya yi mini ƙarya -Ortom


Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue yace takwaransa na jihar Filato, Simon Lalong bai taba yi masa gargadi ba kan dokar hana kiwon dabbobi a fili.

A ranar Alhamis ne Lalong bayyana cewa sai da ya gargadi Ortom kan aiwatar da dokar hana kiwon dabbobi musamman shanu a fili.
Amma da yake magana ranar juma’a lokacin da ya karbi wakilan kungiyar Tuntubar Juna ta Arewa, gwamnan na jihar Benue yace ya tuntubi Lalong bayan da wani ya ja hankalinsa kan maganar.

Gwamnan na Filato ya musalta yin waccan magana.

“Jiya wani yaja hankalina cewa shi (Lalong) yayi maganar cewa ya gargade ni kan kada na aiwatar da dokar da hana kiwo a jihar Benue hakan yasa ni shiga cikin tunanin ko takwara na daga jihar Filato zai iya faɗin haka saboda haka sai nakira shi kuma ya sheda min bai fadi haka,”Ortom yace.

 “Amma daga baya, bayan da na kalli tattaunawar da yayi da manema labarai a gidan talabijin na Channels nayi ƙoƙarin sake kiransa amma yaƙi daga waya ta.”

You may also like