Lauyan Nmandi Kanu Ya Kai Buratai Kara Gaban Kotu 


Ifeanyi Ejiofor, lauyan Nmandi Kanu shugaban kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja da ta umarci babban hafsan sojin Najeriya,Tukur Buratai da ya bayyana inda mutumin da yake karewa yake.

A makon da ya gabata Ejiofor, ya shigar da  kara gaban kotun inda ya nemi ta janye hukuncin da tayi na aiyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar yan ta’adda.

Sojoji sun bayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar yan ta’adda kafin daga bisani gwamnati ta nufi kotu domin halatta aiyanawar kamar yadda doka ta tanadar.

Amma a ranar Laraba, lauyan Kanu ya sake shigar da wata karar inda ya nemi kotun da ta umarci babban hafsan sojin kasarnan da ya bayyana wurin da Kanu yake.

Lauyan yace an yiwa Kanu ganin karshe a ranar ranar 14 ga watan Satumba lokacin da sojoji suka mamaye gidansu dake Afarakwu a Umuahia babban birnin jihar Abia.
Koda a jiya sai da Emmanuel, Wanda kanine ga Kanu ya nemi  sojoji su fito dashi a raye ko a mace.

You may also like