Lebanon: ‘Yan gudun hijirar da suka ce tsintar bola ya fi musu bara a titi



bindigger

Asalin hoton, LEE DURANT / BBC

Bayanan hoto,

Deiri Fayyad, ɗan shekara 26, ya ce da tsintar bola ne kaɗai zai iya ciyar da iyalinsa, ya samar musu matsugunni

Deiri Fayyad yana ta lalube cikin kwandunan shara a Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon don samun robobi da abubuwan da aka zubar masu sauran amfani.

Aiki ne na ƙasƙanci, amma zaɓin da mahaifin ‘ya’ya ukun yake da shi, ɗan kaɗan ne, matuƙar yana son ciyar da iyalinsa.

“Ina fara aiki ne da sassafe, misalin ƙarfe 8:30 kuma nakan yi aiki fiye da tsawon sa’a 12 a rana,” ya faɗa, lokacin da ya ci gaba da dube-dubensa a cikin shara.

Yana amfani da hannuwansa ne, kuma ba tare da tufafin kariya ba, Deiri yakan zura jiki a cikin kwandon shara, ya buɗe ledoji don ganin abin da zai iya samu.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like