Leburori sun kashe abokin ikin su


 

 

Kotun Ebute Meta,ta umarci da acigaba  tsare wasu leburori guda biyu,Ayuba Abume shekaru 32 da Dogo Yakubu 30,  a kurkuku akan kashe wani Mamudu Amidu dan shekara34.masu daukaka kara sunce da Ayuba da Dogo sun tararwa Mamudun ne da duka har sai da suka kashe shi.dalilin kashe shin shine wai Abu ya kai karar Amidu ne wajen Dogo wai Amidu ya sace mai waya jin haka ne Dogo da Abu suka yanke shawarar dukansa amman Amidu ya basu hakuri kuma suka hakura daga bisani makwabtan da suka ji me yafaru suka dage sai an hukunta Amidu.

haka suka tarar wa amidu har da abokan sa Abu da Dogo suka yita dukansa  har sai da yafita hayacinsa da ga bisani yace ga garin ku nan(ya mutu). wannan alamarin ya faru ne a gida me namba 10,layin Prime Adesoji Street,Ogudu GRA phase 11 Ogudu.

 

 

You may also like