Leeds United ta kori kocinta Jesse Marsch



Jesse Marsch

Asalin hoton, Getty Images

Leeds United ta sallami kociyanta Jesse Marsch, bayan kasa da shekara daya yana kan aikin.

Kungiyar ta yi rashin nasara 1-0 a Nottingham Forest ranar Lahadi, kuma wasa na bakwai kenan da Leeds ta kara ba tare da narasa ba.

Hakan ya sa kungiyar take ta 17 a kasan teburi da tazarar rarar kwallaye tsakaninta da ‘yan ukun karshe.

Rabon da Leeds United ta ci wasa tun ranar 5 ga watan Nuwamba.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like